Abubuwan Da Mata Za Su Sha Don Dauwamammiyar Ni’ima

 Abubuwan Da Mata Za Su Sha Don Dauwamammiyar Ni’ima! 



To, Uwargida wannan satin shafin namu zai dan canja salo duk da wadancan abubuwan gyaran jikin ma ko rabin-rabi ba mu gama kawo su ba, amman za mu dan waiwayi wani bangaren, inyaso wani lokacin kuma sai mu dawo bangaren gyaran fata.

Da yawa mata su na yawan kawo min korafin daukewar ni’ima a jikinsu, wato bushewar gaba, da daukewar sha’awa yayin jima’I, wanda yawancinsu su kan ce da ba haka su ke ba; lokaci guda su ka ji sun kasance a hakan.

Yawancin mata rashin kula da kai da rashin sanin irin abubuwan da yakamata su dinga ci domin samun dauwamammiyar ni’ima a jikinsu don samun gamsuwar kawunansu da jin dadin mazajen shi ke haifar mu su da.matsalar daukewar ni’ima da kuma daukewar sha’awa.

Wasu kuma su kan kamu da ‘toilet infection’ ne saboda rashin tsaftar bandaki, wasu ba sa taba kula da gyaran bandakinsu, wasu kuma su kan dauka a bandakin hadaka..

Abubuwan da ya kamata mu mata mu dinga ci, domin karuwar ni’imar jikinmu da da jin dadin mazajenmu:-


Wasu Abubuwan Guda 10 Da Suka Kamata Ma'aurata Su Sani:

A na son mace ta dinga cin daya ko biyu daga cikin wadannan abubuwan kullum a rana; a cikinsu akwai abubuwa masu saukin kudi wadanda duk rashin hadi ki ko rashin halin maigida, zai iya siya, kuma wadannan abubuwa su na kara lafiya da kuzari a jikkunan aluUmma kuma garkuwa ne ga kamuwa da wasu cutukan. Haka kuma ya na karawa mata ni”ima da jin dadi wajen mazajensu.

Wadannan Ba Wasu Abubuwa Ba Ne Illa:

Kankana, Ayaba ,Gwanda, Goba, Lemo, Tumatir, Rake, Aya, Kwakwa, Dafaffiyar gyada, Zuma, Nono, Madara, Madarar Shanu, Gurji, Dabino, Chukwi, Zogale, Ruman, Inibi, Tuffa, Zaitun.

Misali yau idan ki ka sami jikakkiyar ayarki ki ka ci, gobe ki sami raken ki ki sha, jibi ki sami nunannun tumatur dinki manya guda biyu ko uku ki shanye, gata ki sha kankana ko nono. Ki dinga cin abu kala biyu a cikinsu, to wallahi Ina tabbatar mi ki banda ni’ima, hatta fatar jikinki sai ta murje ta goge ta yi kyau.

Sannan wasu daga cikin su a na shan ruwansu domin ni’ima ta musamman ko a sarrafa wani abin da ruwan, don samun dauwamamman jin dadin ma’aurata, kamar:

❑-Ruwan kwakwa


❑-Ruwan zam zam


❑-Ruwan kankana


❑-Ruwan tumatir


❑-Ruwan zogale


❑-Ruwan ruman


❑-Ruwan ayaba


❑-Ruwan guaba


❑-Ruwan dabino


❑-Ruwan rake


❑-Inibi


❍-Ruwan kwai


❍-Ruwan kaninfari


❍-Ruwan itacen baure


❍-Ruwan sassaken gamji


❍-Ruwan madarar shanu


❍-Ruwan zaitun


❍-Ruwan tuffa

Post a Comment

Previous Post Next Post