Wasu Abubuwan Guda 10 Da Suka Kamata Ma'aurata Su Sani:

 Wasu Abubuwan Guda 10 Da Suka Kamata Ma'aurata Su Sani:1: Duk Wanda Zaka Aura Ko Zaki Aura Sunada Nasu Matsalar.

Babu mace ko namijin da za a aura ba tare da yanada ko tanada nata matsalar ba.

2: Duk Wanda Zaka Aura Ko Zaki Aura Baza A Rasa Wani Labari Mara Dadin Ji Akansa Ba Ko Akanta Ba.

Kada mutum yayi tunanin zai auri macen da bata taba laifi ba ko namijin da bai taba yin wani abu a gulmata ba.

3: Duk Wasu Ma'aurata Suna Da Tasu Matsalar.

Kada ku dauka gidan wane ba a samun matsala. Kowa da irin matsalar da yake fuskanta a gidansa na aure, da miji yake hakuri da matarsa ko matar take hakuri da mijinta ko duk ana hakuri ne da juna.

Don haka kuyi kokarin magance matsalar ku da kanku wanda zakuje masa da matsalar ku shima yana da tasa matsalar.

4: Kowa Da Yanayin Zamantakewar Aurensu.

Kada kuce yadda kukaga wasu suna rayuwar aurensu kuma dole haka zakuyi.

5: Daga Ranar Da Aka Daura Muku Aure Daga Ranar Ya Kamata Ku Koyi Hakuri Da Juna.

Shi a aure ba a yawan zuwa ana tonawa juna2 asiri. Dole ne a samu matsala kuma dole ne a gyaran matsalar.

6: Babu Wani Zaman Auren Da Ake Yinsa Babu Magulmata.

Ko kuna zaune kalau ko kuna fada da juna dole sai an samu 'yan gulma da tsaigumi da sai sunce ko ba a tambayesu ba. Don haka sai ku kiyaye.

7: Babu Wanda Zai Ce Allah Ya Bashi Ko Ya Bata 100 bisa 100 Na Irin Wanda Aka Yi Burin Aure.

Shi yasa a aure Allah ne ake baiwa zabi. Sau dayawa ba abunda muke so muke aura ba. Don haka duk wacce ko wanda Allah Ya aura mana mu yi zaman ibada na gaskiya da gaskiya dasu.

8: Aure Ibada Ne:

Dole duk ma'aurata su sani aure Ibada ne, babu wanda za a masa dole yayi aure. Amma duk wanda yayi aure za a masa dole ya kula da auren.

9; Duk Wani Auren Da Aka Daura Ana Burin Mutuwa Zai Raba.

Ba a yin aure da tunanin rabuwa. Rabuwa a aure yana zuwa ne tamkar mutuwa ba a sonshi ba a nemansa.

10: Duk Wani Magidanci Hakkinsa Ne Ya Kulla Da Iyalansa. Duk Wata Mace Hakkinta Ne Ta sauki Nauyin Auren Dake Kanta.

Ba kamar yadda ake cewa aljanar mace na kafafun mijinta ba, Amma ita mace aki sanar da ita aljanar mijinta na kafafuwanta ita ma.

Duk wani daya zalunci wani a zaman aure ko namiji ko mace babu wanda Allah zai kyale. Don haka aljanar kowa na kafafuwan kowa.

Shi dai aure Sunnane na Dukkannin Annabawan, domin Allah SWT Shi Yace dukkanin Annabawansa suna da juriya. Don haka girman aure ya wuce wasa tunanin da ake Yi masa na Jima'i.

Allah babu ruwansa da tambayarka ko tambayar ki dalilin rashin yin aurenka ko aurenki idan ka mutu bakayi aure ba ko kika mutu ba aure. Amma zai tambayeka yadda ka zauna kika zauna da Iyalanka, iyalanki idan mutum ya mutu yana da aure. Don haka aure idan kasan bazaka iya kula da hakkonsa ba rashin yinsa a wajenka, a wajenki shi yafi.

Post a Comment

Previous Post Next Post