Tarihin Ruwan Zamzam Da Kuma Fa'idar Shan Ruwan Zamzam

 Tarihin Ruwan Zamzam Da Kuma Fa'idar Shan Ruwan Zamzam



Annabi Ibrahim عليه السلام

ya zauna tare da matarsa Saratu عليها السلام

a Kasar Falasdinu tsawon lokaci amma ba su samu haihuwa ba.

Ita kuma tana fatan Allah Ya baiwa Annabi Ibrahim عليه السلام wanda zai gaje shi.

Don haka sai ta ba shi Baiwarta mai suna Hajara عليها السلام

  ya aura. 

Sai Hajara عليها السلام

ta haifar masa da mai suna Isma'ila عليه السلام.

Don haka Sai Annabi Ibrahim عليه السلام 

da matarsa Saratu عليها السلام 

sukay farin ciki sosai da samun wannan da.

Sai Allah Madaukakin Sarki Ya umarci Annabi Ibrahim

 عليه السلام

ya dauki matarsa Hajara da jaririnta Ismail ya kaisu inda garin Makka yake a yanzu.

Sai Annabi Ibrahim ya bi umarnin Allah Madaukakin Sarki ya cewa matarsa ta zo ta raka shi unguwa.

Sai ta dauko jaririn nata ta goya shi, ta bi Annabi Ibrahim عليه السلام

suka cigaba da tafiya. Ba ta san inda za a je ba amma saboda biyayya tana biye da shi.

Har saida suka iso daidai garin Makka. A lokacin babu gini ko daya a wajen. Ba mutane, ba bishiyoyi, ba ruwa, ba abinci, ba tsuntsu, ba wata dabba, ba komai a wajen sai Sahara da duwatsu.

Sai Annabi Ibrahim عليه السلام

yay mata umarni ta zauna a wajen.

Sai ta zauna. Shi kuma ya juya yay tafiyarsa.

Sai ta kwalla masa kira ta ce " Ya Annabin Allah!, ka kawo mu nan wajen, ba abinci ba ruwa ba kowa a wajen kuma ka juya ka tafi ka bar mu".

Sai Annabi Ibrahim عليه السلام

ya tasaya, ba tare da ya juyo ya kalleta ba kuma bai ce mata komai ba.

Sai ta sake ce masa " Ko Allah ne Ya umarce ka ka kawo mu nan?".

Sai ya ce mata "E".

Sai ta ce masa "To je ka ba komai. Tunda Allah ne Ya sa ka kawo mu na san zai kula da mu".

Sai Annabi Ibrahim عليه السلام

ya tafi ba tare da waiwayo ya kallesu ba, saboda kada tausayinsu ya kama shi ya kasa zartar da umarnin Allah.

Don haka yay musu addu'a ya wuce abinsa.

Bayan Annabi Ibrahim عليه السلام ya tafi, sai Jaririn Hajara 

  عليها السلام

ya saka kuka, yana bukatar ruwa.

Sai ta tashi ta fara zagayawa cikin Sahara da cikin duwatsu ko za ta samu ruwa amma ko alamar ruwa babu.

Shi kuma jariri yana cigaba da tsalla kuka.

Sai tay ta zagaye tana dubawa.

Da akwai wasu manyan duwatsu da ake kira Safa da kuma Marwa. Sai ta hau kan dutsen Safa ta lelleka ko ina ko zata hango ruwa amma bata hango.

Sai ta sauko ta hau dutsen Marwa ta lelleka ko zata hango inda ruwa yake amma bata hanga ba.

In ta hau ta sauko sai ta zo ta duba yaronta ta sake komawa.

Sai da tay kaikawo tsakanin Safa da Marwa sau bakwai tana hawa dutsinan tana saukowa amma ba ta hango inda ruwa yake ba.

Shi kuwa Jaririn wato Annabi Isma'il عليه السلام

yana cigaba da kuka yana shure-shure da kafafuwansa irin yadda jarirai suke yi.

Tausayinsa ya kama ta ta zauna ta kura masa ido tana jira ta ga yadda Allah Zai yi da su.

Kawai sai ta ga ruwa yana 6ul6ulowa daga inda danta yake shusshura kafarsa.

Sai tay maza ta tashi tana tare ruwan, tana ce masa "Taru! , taru!, taru!"

Ma'ana ruwan ya taru kada ya kwaranye.

Sai ruwan yay ta taruwa yana dada yawa har sai da ya zama kogi.

Da yaren su Hajara عليها السلام

idan za a cewa abu ya taru sai a ce 'Zam'

Don haka sai tay tacewa "Zam!, zam!, zam".

Shi kuwa ruwa yana taruwa.

Sai Hajara عليها السلام

ta baiwa `Dan ta ruwa ya sha kuma ta samu ruwan amfani.

Sai ga tsuntsaye ma sun fara zuwa kogin suna shan ruwa.

Ana nan watarana sai wasu Larabawa da ake kira Jur'hum suka zo wucewa ta Sahara, sai suka hango tsuntsaye suna shawagi a sararin Samaniya. Sai sukay mamaki. Domin sun san ba a ganin tsuntsaye a Sahara, saidai idan akwai ruwa a wajen.

Saboda haka sai suka je suka duba. Sai kuwa suka samu wannan Baiwar Allah ita kadai da Jaririnta. Sai su ka tambaye ta labarinta ta gaya musu.

Sai suka ce "To za mu zauna tare da ke a wannan guri amma wannan ruwan na ki ne, tunda ta dalilinki ya samu".

Don haka sai suka zauna a wannan waje. Idan suna bukatar ruwa sai su baiwa Hajara abinci ita kuma ta ba su ruwa

FA'IDODIN RUWAN ZAMZAM GUDA 36.

1-ZAMZAM, MALAIKA JIBRILUNE YA TONA RIJIYARSA.

2 ANNABI ISMAILA NE YA FARA SHAN RUWANZAMZAM.

3 ZAMZAM SHINE ASALIN KAFUWAR BIRNIN MAKKA


4 DA ZAMZAM AKA WANKE ZUCIYAR ANNABI MUHAMMAD صلى الله علي وسلم.


5 BABU RUWAN DA YA FISHI DARAJA, A DORAN KASA. 


6 ANNABI MUHAMMAD صلى الله عليه وسلم YA SHA RUWAN ZAMZAM.


7 ANNABI MUHAMMAD صلى الله عليه وسلم YA ZUBASHI A JIKINSA.


8 ANNABI MUHAMMAD صلى الله عليه وسلمYAYI GUZIRIN SA ZUWA MADINA.


9 ANNABI MUHAMMAD صلى الله عليه وسلم 

YACE ,RUWAN ZAMZAM ZAKA SAMI

BUKATAR DA KASHA SHI, SABODA ITA.


10 NANA AISHATU رضي الله عنها

, TANA GUZIRIN ZAMZAM. 


11 SABODA DARAJAR RUWAN ZAMZAM, MALAMAI

SUKAYI SABANI GAME DA WANKA DA SHI, DA

ALWALA DA TSARKI DA WANKE NAJASA.


12 SABODA DARAJAR RUWAN ZAMZAM MALAMAI

SUKAYI SABANI DA SHI DA RUWAN KAUSAR WANNE

YAFI DARAJA?!


13 MAL IBN HABIB BAMALIKI YACE

 "ANSO GA WANDA

YAYI HAJJI, YA YAWAITA SHAN ZAMZAM, SABODA

SAMUN ALBARKA, YAYI ALWALA YAYI WANKA.


14 SHAIK ALBANIY YACE, YA KAMATA ALHAJI, YAYI

GUZURI DA ZAMZAM, DOMIN NEMAN ALBARKA,DOMIN

ANNABI MUHAMMAD صلى الله عليه وسلم

YAYI GUZIRIN SA A CIKIN GORA DA SALKA ZUWA MADINA, YANA ZUBAWA MARASA LAFIYA YANA

SHAYAR DA SU.


15 MAL ANNAWAWIY, YACE , MAZAHABARMU KAMAR

TA JAMHURIN MALAMAI, BABU LAIFI AYI WANKA DA

ZAMZAM, KUMA AYI ALWALA.


16 MAL WAHAB IBN MUNABIH YACE: ZAMZAM ABIN SHAN MASU NAGARTA, YANA TSAYAWA A MATSAYIN

ABINCI DA ABIN SHA, KUMA WARAKA DAGA LARURA.


17 MAL KHALIL, A CIKIN MUKTASAR YACE : YANA DAGA

CIKIN ABINDA AKE SO GA ALHAJJI, YA YAWAITA SHAN

ZAMZAM.


18 ACIKIN SHARHIN AN SANHURIY YACE: YANA DAGA CIKIN ABINSO, YAWAITA SHAN ZAMZAM, DA ALWALA,

DA WANKA, DA YAWAITA ADDUA A LOKACIN SHAN

ZAMZAM GA ALHAJI.


19 AL IMAM SHAFII, YACE: MUSTAHABBI NE YAWAITA

SHAN ZAMZAM.


20 MALAMAN SHAFI'AWA SUNCE: MUSTAHABBI NE SHAN ZAMZAM, DA YAWAITA SHAN SA, KUMA ANSO MUTUM

YA SHIGA CIKIN INDA RIJIYAR ZAMZAM TAKE, YA KALLI

RUWAN, YA DEBO DA GUGA, YA SHA YA ZUBA AKANSA.

DA FUSKARSA, DA KIRJINSA, KUMA YAYI GUZURI DA

SHI.


21 MAL HASANUL BASARI YACE: IDAN AN SHA RUWAN ZAMZAM AYI ADDUA, YANA CIKIN GURARE 15 DA AKE

SA RAN KARBAR ADDUAR MASU AIKIN HAJJI, SUNE

WAJAN DAWAFI, MULTAZAM, KARKASHIN INDARARO,

CIKIN KAABA, ZAMZAM, KAN SAFA, KAN MARWA,

CIKIN SAAYI, BAYAN MAKAMU IBRAHIM, MUNA, FILIN

ARFA, MUZDALIFAH, JAMRA GUDA BIYU TA FARKO DATA BIYU ANA TSAYAWA AYI ADDUA.


22 ABDULLAH DAN ABBAS RA, IDAN YA SHA ZAMZAM

SAI YAYI ADDUA YACE: YA ALLAH KA BANI ILMI MAI

AMFANI , DA ARZIKI MAI YALWA, DA WARAKA DAGA

DUKKAN LARURA.


23 ABDULLAH DAN MUBARAK IDAN YA SHA ZAMZAM SAI YA KALLI GABAS YAYI ADDUA YACE: "YA ALLAH

MANZON ALLAH صلى الله عليه وسلم

YACE, RUWAN ZAMZAM ZAKA

SAMI BUKATAR DA KASHA SHI SABODA ITA, TO GANI

NA SHA, KA RABANI DA KASHIRWA RANAR

ALKIYAMA".


24 RUWAN ZAMZAM YANA MAGANIN ZAZZABI DA MASHASHARA.


25 RUWAN ZAMZAM YANA ZAMA DALILIN KANKARE

ZUNUBI WANDA YASHA DA NIYAR TUBA


26 RUWAN ZAMZAM YANA KARA KARFIN HADDA,

WANDA YAKE SHA DA NIYAR HAKA, KAMAR YADDA AL

IMAM SUYUDIY YAYI YA ROKI ILMIN FIQHU DA HADIS. 


27 RUWAN ZAMZAM YANA KARA KARFIN MUTUM WAJAN

MU'AMALA DA IYALI.


28 SHAN ZAMZAM ALAMACE TA IMANI.


29 RUWAN ZAMZAM YANA MAGANIN YAWAN JIRI.


30 WANKE FUSKA DA ZAMZAM YANA KARA KARFIN

IDO. 


31 SHAN ZAMZAM YANA KARA KARFIN ZUCIYA.


32 SHAN ZAMZAM YANA TAFIYAR DA YAWAN FIRGICI

DA TSORO.


33 SHAN RUWAN ZAMZAM YANA RAGE GIRMAN KAI.

YANA HORE ZUCIYA.


34 KALLON RUWAN ZAMZAM YANA DA AMFANI. 


35 MAL ALBANIY YACE: YA GAMU DA WATA LARURA

WANDA LIKITA YACE SAI ANYI MASA AIKI, AMMA

KAFIN ZUWAN RANAR AIKIN, DA YA DUMFARI SHAN

RUWAN ZAMZAM, DA LOKACIN AIKIN YAYI, SAI AKA CE

BABU CUTAR YA WARKE. 


36 MAL IBNUL QAYYIM YA KAWO A CIKIN LITTAFIN SA. ZADUL MAAD, CEWA: YA GAMU DA LARURA A MAKKA

YA RASA LIKITA, SAI YA DEBI RUWAN ZAMZAM YANA

KARANTA FATIHA YASHA, NAN TAKE YA WARKE.

.

.

Daga shafin Bashir Halilu Tarbiyyah Islamiyah.

Post a Comment

Previous Post Next Post