Abubuwan Da Zasu Iya Faruwa Dake Idan Kika Daina Jima'i:

 Abubuwan Da Zasu Iya Faruwa Dake Idan Kika Daina Jima'i:



Wasu saboda sun rabu da mazansu ne. Wasu mazan basa tare dasu. Wasu matan kuma haka nan kawai mazan suke daina saduwa dasu ko kuma su da kansu su nuna basu da sha'awar Jima'i da mazajensu.

 Ko ma dai menene dalilin dake hanaki Samun biyan bukata irin na Jima'i. Kina da nakasu saboda rashin yinsa a lafiyar ki.

Ko wacce mace da irin hakurinta na tsawon lokacin da zata iya dauka ba tare da Jima'i ba.

A wannan darasin mun binciko muku illar da rashin Jima'i yake haifarwa lafiyar duk wata mace data saba da shi yanzu kuma bata samunyi.

Da zaran mace ta daina samun Jima'i kaman yadda ya kamata za a sameta da yawan fushi, da kuma kasala.

Haka nan kawai abu zai rika bata mata rai ba tare da wani dalilin ba. Sannan ako da yaushe jikinta babu karfi. 

Baya ga hakan masanan sun tabbatar da cewa rashin samun yin Jima'i ga mata yakan sasu saurin mantuwa da kuma disashen kwakwaluwa.

Tunani da hankalin macen da take yin Jima'i yafi na wacce bata samu.

Kaman suma maza. Matan da basa samun gudanar da Jima'i akai akai a yawancin lokuta suna cikin cuta. Ciwo mai sauki irin mura idan ya kamata macen da bata samun sabis sai ya jima bai warke ba. Amma macen da take samu nan take yake bacewa.

Kamuwa da cutuka cikin sauki yafi addabar macen da bata Jima'i.

Farjin macen da bata samun Jima'i zai tsuke, kofar gabanta zai dawo karami, yadda duk lokacinda za a sadu da ita sai taji ciwo.

Haka nan macen da ba a yawan saduwa da ita tana iya fiskantan bushewar farjinta ko kuma zuban ruwa a gabanta a wasu lokutan.

Macen da bata samun namiji a duk lokacinda zata yi al'ada sai ya zo mata da zafi da kuma ciwo ba kamar macen da take samu ba.

Idan mace ta dauki tsawon lokaci babu Jima'i takan iya daina jin sha'awar Jima'i a tare da ita. Zata ji sha'awa ya dauke mata. Duk wannan illar rashin sabis ke kawosu.

Cardiovascular wani cuta ne inji masana dake iya kama duk wata mace data jima bata hau network ba. Sukace shi yawan saduwa ga diya mace yakan taimakamata wajen kubuta daga kamuwa da cutar zuciya. 

Duk da wadannan matsalolin da rashin samun jimai kan iya haifarwa ga lafiyan mace. Akwai kuma wasu alfanun da mutum zai iya samu idan ya daina Jima'i inji su masanan. Wadanda nan gaba zamu kawo su. Idan Allah Ya bamu ikon.

Yanzu dai Maza da Mata kunji illar da rashin Jima'i ke iya jawowa Dan Adam ga lafiyarsa. Da fatan za a bi hanyoyi na halasa wajen yin Jima'in akai akai.

Post a Comment

Previous Post Next Post