Hanyoyi 5 dake hana furfura fitowa a jikin mutum:

 Hanyoyi 5 dake hana furfura fitowa a jikin mutum:



A da tsofaffi ne ake dangantawa da farin gashi a ka, wato Furfura, amma yanzu abin ya canza, sai kaga har jariri ma ya zo duniya da farin gashi a ka.


A dalilin haka ne wasu masana suka gudabar da bincike inda suka musanta cewa ba duka Furfura bace take zama halitta daga Allah, akwai abubuwan da ke kawo su.


Malaman sun bayyana cewa fitowar furfura a jiki ya rabu kashi biyu ne; Akwai wanda nasu halittace daga Allah sannan da wanda yake fitowa saboda rashin garkuwar jiki mai karfi.


Likitocin sun ce an halici jikin mutum da garkuwa da suke taimakawa wurin kare mutum daga kamuwa da cututtuka.


‘‘Furfura kan fito a jikin mutum musamman yaro karami idan garkuwar jiki nasa bashi da karfin kare shi daga kamuwa da cututtuka.”


Domin guje wa irin haka malaman sun bayyana wasu hanyoyin da za su taimaka wa mutum guje wa samun garkuwar jiki mara karfi.


Ga hanyoyin:


1. Yawaita cin abincin dake dauke da sinadarin dake karfafa garkuwar jiki kamar su ganye, kayan lambu, madara, kifi, da sauransu.


2. Samun isasshiyar hutu musamman ga wadanda suke ganin cewa hutawa lalaci ne.


3. Rage damuwa domin yawan damuwa na kawo tsufa da wuri.


4. A dunga motsa jiki domin yana taimakawa wurin bunkasa garkuwar jiki.


5. A rage cin abincin kamar shan giya, yawan cin maiko, kanzon tukunya da makamantan su.


6. A dunga tsaftace jiki, muhalli da abinci.

Post a Comment

Previous Post Next Post