Yadda Za Ki Kula Da Fata Mai Maiko A Wannan Lokaci Na Zafi

 Yadda Za Ki Kula Da Fata Mai Maiko A Wannan Lokaci Na ZafiFata mai maiko kan ba wa wasu mata matsala musamman saboda yadda yake yawan bata musu kwalliya.

Mun kawo muku wasu hanyoyi da za ku yi amfani da su don kawo karshen wannan matsala kamar haka:

Na Farko shi ne yawan yin ‘facial mask’ da kwai.

Yadda ake yin ‘facial mask’ shi ne za ki fasa danyen kwai, ki cire kwanduwar ki bar farin.

Sai ki lullube fuskarki da ‘tissue paper’ sannan ki yi amfani da burushin shafa kayan kwalliya kina dangwalar ruwan kwan kina shafawa a tissue da ki ka lullube fuskarki da ita har sai ko’in a fuskarki ta jike da ruwan farin kwan.

Ki bar shi na tsawon minti 10 zuwa 15 sannan ki wanke da ruwan dumi.

Hanya ta biyu ta magance maikon fuska ita ce yawan goge fuskarki da lemon zaki ko lemon tsami akalla na minti bakwai zuwa goma kafin shafa kayan kwalliya.

Yin hakan na magance maikon fuska da kuma sanya laushi da shekin fata.

A lura cewa idan aka yi wannan hadin to ba kya bukatar wanka da sabulu, amma za ki iya amfani da ruwan sanyi ko na dumi wajen dirje jikinki da kyau ta yadda kwabin zai wanku sosai.

Na uku shi ne duk man shafawa ko ‘cream’ din da za ki yi amfani da shi ya zama an rubuta FOR OILY SKIN (Domin masu maikon fata) ko kuma FOR ALL SKIN TYPES (domin kowace irin fata) a jiki.

Kar ki biye masa saboda wa dadin kamshinsa ko don shi ake yayi ko kuma tsadarsa.

Wadannan abubuwan za su sa fatarki ta daina maiko kuma ko da kin yi kwalliya, babu ruwanki ballantana maikon fuska ya bata miki shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post