Yadda Ake Haɗin Man Tafarnuwa, Ayi Kasuwanci Ko Magani Dashi

Yadda Ake Haɗin Man Tafarnuwa, Ayi Kasuwanci Ko Magani Dashi



Yin man Tafarnuwa abu ne mai sauƙin gaske. 

   Kawai ka samu Tafarnuwa adadin yadda kake bukata, misali gwangwani ɗaya, wacce ba a ɓare ba. Sai ka samu Man Zaitun ko Man gyaɗa Mai kyau kamar kwalba uku zuwa biyar. 

   A wanke tafarnuwar sosai, a gyara ta, a cire datti. Ba lallai sai an ɓare ta ba. Daga nan sai a daka ta ko a jajjaga ta, sai a zuba acikin Man Zaitun ko Man Gyaɗa ko kuma dukkan Man da aka tanada.

   A ɗora akan wuta, a sa wuta kaɗan-kaɗan har sai tafarnuwar ta fara canjawa zuwa ruwan ƙasa amma kada a bari man yay ta tafasa sosai. 

   Daga nan sai a sauke man daga kan wutar, a bar shi ya huce da tafarnuwar a ciki. A samu kwalba a zuba a ciki, a rufe ta da kyau, duk sanda za a yi amfani da shi sai a dinga tsiyaya. Sannan za a iya tacewa, sai a ajjiye tataccen man Tafarnuwar.

   Kada ku manta dai na kawo muku fa'idoji da kuma amfanin man tafarnuwa wajen kyauatata lafiya da kuma gyara kayan amfani tun a baya. Mai son ya gani zai iya dubawa shafina.

Post a Comment

Previous Post Next Post