Dalilin Da Yasa Yan Sanda Suka Kama Amal Umar Jarumar Kannywood

Dalilin Da Yasa Yan Sanda Suka Kama Amal Umar Jarumar Kannywood “Saurayin jarumar Kannywood Amal Umar ake zargi ya damfari wani Alhaji Naira miliyan 40 ya tura milyan 13 acikin asusun ta.

Rundunar ƴan sanda ta ce wani Alhaji ne ya kai ƙorafin cewa wani mutum ya damfare shi Naira miliyan 40 za su yi sana'ar doya sai ya gudu bayan ya karɓi kuɗin. Da ƴan sanda suka fara bincike sai suka samu cewa an tura Naira miliyan 13 zuwa account ɗin Jarumar fim Amal Umar. 
Sai ƴan sanda suka gayyato ta kuma ta tabbatar cewa mutumin da ake zargi saurayinta ne. Bayan an fara bincikenta har an karɓi motar ta sai ta lallaɓo ta nemi baiwa wani Jami’in ɗansanda cin hancin dubu ɗari biyar N500,000 don ya karɓo mata motar ta sannan ya kashe case ɗin. Nan ne fa ƴan sanda suka yi mata ƙofar rago bayan ta faɗa tarko sai suka gurfanar da ita a kotu.... -inji Rundunar ƴan sanda.

Post a Comment

Previous Post Next Post