Sabon Haɗin Ni'ima Na Kwakwa, Dabino Da Aya

Sabon Haɗin Ni'ima Na Kwakwa, Dabino Da AyaGa wasu daga cikin amfanin sinadaran da aya ta kunsa:

Tana dauke da sinadaran ‘magnesium’ da ‘calcium’ da kuma ‘iron’.

-Tana samarwa jiki sinadarin ‘protein’ da kuma lafiyayen kitse.

-Tana kunshe da sinadarin ‘bitamin B’ wanda ya ke amfanar da fata da gashi da kuma farce.

Don samarwa da jiki sinadaran ‘bitamin’ da ‘minerals’, ya na da kyau a rika cin ‘gram’ 70 zuwa 50 na Aya a kullum.

-Aya tana da amfani saboda tana kara karfin garkuwar jiki sinadarin ‘carbohydrates’.

-Idan kana yawan amfani da ita, za ka gano cewa ba ka yawan rashin lafiya kuma za ka ji dadi sosai.

-Aya na inganta yanayin da mutum ke ciki, tana tsawaita kuruciya, tana karfafa yanayin gudanar jini sannan tana kara kuzari na zahiri da na boye.

-Haka kuma aya tana da amfani ga sha’anin da ya shafi ciki da hanji, tana dauke da sinadarin da ke hana cushewar ciki da kuma kumburi.

-Aya na taimakawa wajen rage sinadarin kwalestaral (maikon cikin jini) marar kyau a cikin jini.

KWAKWA

Kwakwa na daga cikin ‘ya’yan itatuwa masu matukar amfani ga rayuwar dan’adam, kamar yadda masana a fannin kiwon lafiya suka bayyana.

Hakan kuwa in ji masana, ba ya rasa nasaba da irin sinadaran da Allah ya saka a cikin ta ne.

Kwakwa na dauke da ruwa, da kuma mai cikinta, baya ga hakan ana bare kwansonta a ci.

Kwakwa ta rabu kashi biyu, akwai kwakwar manja kana akwai kwakwa wacce ba ta dauke da manja.

Dukkanin nau’o’in kwakwa dai na dauke da sinadarai da suke da matukar amfani ga rayuwar dan’adam, kamar yadda masana suka bayyana.

Amfanin Kwakwa

Wasu daga cikin amfanin Kwakwa ga rayuwar dan’adam sun hada da:

-Kwakwa tana dauke da sinadaran da ke kashe kwayoyin cuta da suka hada da bacteria, da birus da makamantansu, don haka tana kara lafiyar garkuwar jikin dan’adam.

Masana sun bayyana cewa ruwan kwakwa yana kara lafiya da kuzari a jikin dan’adam.

-Kwakwa na dauke da sinadaran bitamins wadanda ke taimaka wa sassan jikin dan’adam wajen saurin narkar da abinci.

-Tana taimaka wa masu dauke da cutar suga (diabetes), kana tana samar da garkuwa ga wadanda basa dauke da cutar.

-Tana rage barazanar kamuwa cutar kansa (cancer) a jikin dan’adam. In ji masana.


Yadda Ake Sarrafa Kunun Dabino Da Kwakwa Da Aya

Bayan da binciken masana ya yi nisa game da amfanin ‘ya’yan itatuwa, da ganyaye da sauran tsirrai a fadin duniya, yanzu haka akwai hanyoyi da dama da ake hadawa da kuma sarrafa su ta yadda za su amfani a jikin dan adam a fadin duniya.


Yanzu haka a kan hada Kwakwa da Aya da kuma Dabino a sarrafa su ta hanyar markade, wanda a yankin arewacin Nijeriya ake kira kunu.


Yayin da wasu su kan sarrafa su kuma su rika shan wannan hadi na kunu a matsayin nishadi, ko a lokutan bukukuwa, wasu kuwa suna yin sa da gaskiyar niyyar cewa akwai amfanin da zai musu a jiki.

Ga yadda ake sarrafa su:

Kayan hadi:

Dabino (daidai gwarwado)

Kwakwa ( guda biyu ko daya)

Aya (daidai gwargwado)

Kayan kamshi (don karin armashi)

Sukari (idan ana bukata)

Madara (idan ana bukata).

Matakan sarrafawa

A wanke Dabinon sosai

A fasa kwakwa a tsiyaye ruwan a shanye ko a sha da madarar ruwa.

Za a hada a markade Kwakwar da Dabinon da Ayar, sai a tace da rariya.

Za kuma a iya zuba madarar ruwa a sha, ko kuma haka nan.

Amfanin hadinsu duka (Kunun aya) a jikin dan adam.

Duk da cewa har yanzu akwai mutane da dama da ba su gane muhimmancin amfanin shan kunun Aya ba, inda wasu kan dauka abin sha ne kawai ko kuma maganin yunwa ko kayan marmari, yayin da wasu kuma kayan zaki suka dauke shi.

Galibi dai kunun ayar a kan hada ne da kwakwa da dabino don inganta dandano da kuma amfaninsa.

Shi ya sa daukacin hadin ake kiransa da kunun aya, duk da cewa ba aya zalla kadai ya kunsa ba.

Yawanci an fi sarrafawa a kasar Hausa, inda a kan yi amfani da shi wajen tarbar baki, ko lokacin bukukuwa.

Sai dai kuma yanzu haka a bisa kara zurfin binciken kimiyya da masana suka yi yana nuna cewa wannan hadi na dabino da kwakwa da kuma aya, ya wuce yadda aka dauke shi, saboda dimbin amfanin da suke da shi musamman idan aka sarrafa.

Baya da lafiyar jikin dan adam, masana sun yi ittifakin cewa kunun ayar yana da matukar muhimmanci ga ma’aurata musamman mata.

Masana harkokin zamantakewa da malaman addinai musamman na Musulunci za ka ji suna yawan fadakarwa game da muhimmancin shan ‘ya’yan itatuwa ciki har da su Aya, da Dabino da kuma Kwakwa wajen kara inganta zaman aure tsakanin ma’aurata.

Yanzu haka kuma akwai kasidu da mujallu na kiwon lafiya a kasashe daban daban da ke bayyana muhimmancin aya da dabino da kuma kwakwa a jikin dan adam, musamman ma’aurata.

Kan haka ne ya sa za ka ga irin nau’ukan wadannan l cimaka ke da matukar tasiri da kuma karbuwa a tsakanin al’umma musamman a kasashen Afirka.

Galibi yanzu ba ka rasa ire-iren wadannan cimaka a cikin gidajen mutane a ko da yaushe, saboda wayewa game da amfanin da suke da shi a jikin dan adam.

Za kuma ka ga ana sayar da su a kasuwanni fiye da yadda aka saba gani a shekarun baya.

Hakan kuma ba ya rasa nasaba da rashin sanin amfaninsu a baya, da kuma tunanin cewa irin wannan cimaka ta masu karamin karfi ce ko kuma mazauna karkara wadanda kan su bai waye ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post