Alfanun Yin Jima'i Akai-akai Ga Mace Mai Ciki

 Alfanun Yin Jima'i Akai-akai Ga Mace Mai CikiBa kamar yadda wasu ke tunani ba. Jima'i da mace mai dauke da juna biyu yanada mahimmanci ga ita mai ciki cewar masana.

Ga wasu alfanun da masana suka kawo su ga macen da ake Jima'i da ita idan tana da ciki.

1:Yakan Sa Haihuwa Cikin Sauki: Masana sukace macen da ake yawaita kwanciyar aure da ita bayan ta samu ciki, zata haihu cikin sauki ba tare da doguwar nakuda ba.

Wannan yasa suka baiwa ma'aurata shawaran cewa, kada su sausautawa Jima'i koda kuwa gobe ne macen ake saran zata haihu.

2: Samun Bacci: Jima'i da mace mai ciki yakan sata ta samu bacci mai dadi a duk lokacinda aka sadu da ita.

Ana kammala saduwa da mace mai ciki zata samu wani bacci mai dadin gaske da zata manta duniyar datake ciki.

Don haka ma'aurata kada suyi kasa a gwaiwa wajen Jima'i da ciki.

3: Yana Warware Gajiya: Duk irin gajiya ko damuwa da mace mai ciki take da shi ana saduwa da ita zata ji watsai inji masana.

Wannan yasa duk wata mace mai ciki yana dace a yi Jima'i da ita a lokacinda jikinta yayi laushi ko kuma ta shiga wata damuwa.

4: Narkar Da Kitsai: Masana sukace duk mace mai ciki da ake yawan saduwa da ita kitsai ba zai taru mata a jikinta ba.

Kowa dai yasan illar da kitsai yake dashi a jikin mutum. Amma ita mace mai ciki ta hanyar Jima'i zata samu waraka matsalar kitsai a jikinta. 

5: Maganin Hawan Jini: Duk wata mace mai ciki akwai yiwuwar ta kamu da cutar hawan jini. Amma idan har tana baiwa mijinta gabanta akai akai da cikin, bazata samu wannan matsalar na hawan jini ba inji masana.

Wadannan sune wasu daga cikin alfahun yin Jima'i da mace mai juna biyu kamar yadda likitoci suka tabbatar.

Sai dai kuma yana da kyau maza su fahimta, akwai wasu matan da kwatakwata basa son yin Jima'i idan suna da ciki, idan matarka tana cikin irin wadannan matan, kada ka takura kace dole sai kunyi. Kawai idan tana sha'awar yin Jima'i da ciki to kada ka saurara mata domin samun lafiyanta ne hakan. Idan kuma bata so, sai kayi hakuri, idan kana da wasu matan sai ka wuce acan, idan kuwa kai aminin gwaro ne, sai ka hakura har bayan ta haihu tayi wanka.

Allah Ya sa a rabu lafiya. Allah Ya albarkaci abunda za a haifa

Post a Comment

Previous Post Next Post