Hanyoyi Goma (10) Wanda Za A Bi Don Gyaran Jiki

 Hanyoyi Goma (10) Wanda Za A Bi Don Gyaran Jiki A Lokacin SanyiBarkanmu da sake kasancewa da ku a wannan fili namu na kwalliya. A yau na kawo muku hanyoyi goma wanda za a bi don gyaran jiki ba tare da an kashe kudi a shagon kayan kwalliya ba. Ya kamata mata su koyi dabaru da dama domin taimaka wa maigida. Idan maigida ya saba ba da kudin sayan kayan kwalliya, ranar da babu kuma sai a hakura a gwada daya daga cikin ababen da muke kawo muku na gyaran jiki. A sha karatu lafiya.

1- Idan ana so a gyara gashi za a iya hada ayaba da kwai sai a kwaba su sosai sannan a shafa a gashi a jira na tsawon mintuna sha biyar (15) zuwa talatin (30) sannan a wanke.

2- Domin gyara farce, za a iya tsoma hannu a cikin man zaitun na tsawon mintuna biyar (5) sannan sai a cire a kullum. Farce zai yi matukar kyau sosai.

3- Ana amfani da zuma mai kyau domin samun fuska mai santsi da laushi. Ana shafawa a fuska a jira na tsawon mintuna goma sha biyar (15) zuwa ashirin (20) sannan a wanke da ruwan dumi. A gwada wannan hadin sau daya ma a sati za a ga canji.

4- Ana amfani da ruwan amfuna da ruwa ana wanke kai. Yin hakan na cire dattin da ke makale a gefen gashin kai.

5- Domin masu yawan shafe-shafe za su iya yanka lemon tsami biyu sai su rika shafawa a inda ya yi duhu. Yin hakan a kullum na haskaka bakin da ya bayyana a wasu gabbai ko sassan fata.

6- Domin samun fatar jiki mai sulbi, za a iya amfani da man zaitun da gishirin rafi a kwaba sai a rika dirzawa a fatar jiki a kalla sau uku a sati.

7- Man kwa-kwa na matukar gyaran zubewar gashin ka. Za a iya shafa man kwa-kwa a fatar ka, sannan a shafa a jikin gashin. A bari ya jima kamar na awa daya sannan a wanke.

8- Maza masu son man gyaran gemu, za su iya amfani da man kwa-kwa.

9- A samu lemon tsami sannan a zuba zuma a kai. Sannan a rika shafawa a kan kurajen fuska. Yin hakan na kashe su sosai.

1o- Man zaitun na sanya santsin fata idan an kasance ana yawaita shafa shi a koda yaushe a matsayin man fata


Post a Comment

Previous Post Next Post