Amfanin Shan Nonon Akuya Guda Goma Sha Biyar

 

Amfanin Shan Nonon Akuya Guda Goma Sha Biyar

Akuya wacce muka sani a kasar Hausa,ana kiranta da GOAT a harshen Ingilishi.Takasance daya daga cikin dabbobin da ake kiwo a sassa daban daban a fadin duniya kama daga kasashen Africa,kasashen Turai dana Larabawa.

Amfanin naman Akuya zai iya kasancewa dai dai dana sauran dabbobin da ake ci,amma kuma amfanin nononsu ya banbanta.

Akoi dabbobin da yakasance ana cin namansu amma kuma ba a shan nononsu,misali tunkiya.Ana cin naman tunkiya sai dai kuma ba a shan nononta.

Nonon tunkiya baya kashewa koda an sha sai dai kuma akoi wasu illoli na daban da yake haifarwa.Yana haddasa zafin ciki da taurin rai da kekeshewar zuciya wanda ko kashe mutum za ayi to ba zai gudu ba kuma bazai kokaba.wannan baya rasa nasaba da dabi'un tunkiyar domin yana da wahala kaga inda za a yanka tunkiya kaji tana kuka.kuma komai wahalar da tasha ba zaka ji tana qara ba asali idan baka gani ba sai dai ka iske ta yi mosai akan igiyarta.


Haka kuma kimiyya bata gano wani alfanon dake tattreda shan nonon tunkiya ba,amma kuma ta zayyano dimbin amfanin nonon shanu dana awaki.


A lokacin manzon Allah (s.a.w) an ruwaito cewa fiyayyen halitta ya sha nonon akuya.

Wannan nuni na musamman ga musulmai cewa shan nonon akuya halal ne kuma baya cutarwa.


Dukda yake wani baya iya shan nonon akuya,sai dai na shanu.koma dai an sha to ba wata illa da yake haifarwa.


Glass daya ko kuma ince cup daya na nonon Akuya na daukeda  

calories guda 168.

Saturated fat kusan grms 6.5.

grm 11 na carbohydrates

grm 10 na protein sai 

milligrams 27 na cholesterol(good cholesterol).

grams 11 na sugar

milligrams 12 na sodium


sai minerals din dake kumshe da nonon akuya kamar haka : milligrams 327 na calcium

millilligrams 271 na phosphorus

milliligrams 342 na maganesium

sauran sun hada da copper da zinc da fluoride da niacin.


Sai vitamin A,

vitamin B,vit B1,B2 

vit.D

vit.B6.

Folate

vit B12

Betaine


Da wadannan sinadiran dake kumshe da nonon akuya a fili yake nonon Akuya ya dara na shanu amfani,dukda yake kitsen dake a cikin nonon akuya ya dara na nonon saniya yawa,sai dai shi na nonon akuya nan take yake narkewa yabi jiki baya dasqarewa sa6anin na saniya dake daukar lokaci mai tsawo.kuma na akuya good cholesterol ne amma na saniya idan yaiyi yawa to yana da illa.

Haka kuma,ga masu fama da matsalar nan ta lactose intolerance wadanda shan madara kan kumberawa ciki to nonon akuya baya da wannan matsalar.Asali shan nonon akuya yana succe kumburin ciki.


Nonon akuya na kumshe da sinadiran dake busa garkuwan jiki (immunity) wadanda sune ke da alhakin yaqi da kwayoyin cuta wadanda idan su kayi rauni to cuta zata fi karfin jiki.


nonon akuya na maganin cutukan ciki(gastro intestinal diseases).kumburin ciki,ciwon ciki,kukan ciki,murdawarsa da kuma yawan tashin zuciya.


Nonon akuya na gyara fatar jiki(skin moisturizer).shi yasa kuke ganin fararen buzayenda ke shan nonon awaki kamar Turawa.


Idan kitse yayi maka katutu a jiki to ka lazimci shan nonon akuya zai narke maka da bad cholesterol.


Idan kana son rage nauyin jiki ko qiba to ka nemi nonon akuya lafiyayya ka fake sha.


Mai fama da qaramcin jini ko karamcin sinadiran iron to ga natural blood tonic.ka fake shan nonon akuya bayan shekara daya sai kayi mamaki.


Domin samun karfin kassan jiki kamar buzayen nan dake kokowa a Tawa dake a Nijar republic

sai a fake shan nonon akuya.


Nonon akuya na kare zuciya daga wasu cutukan da bamu da masaniya akansu.

Yana rage damuwa da yawan bugun zuciyar dan akoi phosphorus masu yawa a cikinsa.


Nonon akuya protein ne.shi kuma protein shi ne ke gina jiki kama daga cells,tissues,muscles da kuma bones.


Nonon akuya na wujuwuju da ciwon suga amma kuma akoi yanda za a sarrafa shi.


Macen dake fama da bushewar gaba,wacce take jin kanta ba ni'ima wani binma sai an shafa mai sannan a iya saduwa to ga magani kuma garanti.sai a nemi ridi mai kyau a hada da cumin extract kadan sai a dama a misalin rabin cup sai ya koma mai kauri sosai sannan.haka kuma za'a soya nonon da xx leaf da albasa sai ya soyu sosai sannan a ci.a fake yin haka tsawon sati daya kawai.wallahi za a godewa Allah da kuma mai shafin ciwo da magani.


Nonon akuya yana kara kaifin basira(sharp brain)

yana maganin shawara

(jaundice). kai hartama da ciwon tarin tibi da kuma ciwon hanta.


Sai dai kuma idan za a shayarda jinjiri to kada a bashi nonon akuya,abu mafi kyau shi ne a bashi cow milk.


 

Mai neman magani ko shawara ko tattaunawa kan wata matsala to sai a neme mu ta nambar da muka bayar.

Alhamdulillah.

Post a Comment

Previous Post Next Post