Yadda Ake Gyaran Gashi Yayi Kyau Sosai da ruwan Shinkafar da in kin wanke kike zubarwa.

 Yadda Ake Gyaran Gashi Yayi Kyau Sosai da ruwan Shinkafar da in kin wanke kike zubarwa.Gashi Dai Abu Ne Mai Karawa Mata Kyau Sosai, Wanda Har Gasa Mata Keyi Dashi.


Duk Tarin Gashinki Idan Baki Iya Gyarawa Ba Sai Ya Zube Ko Ya Lalace, Wannan Hanya Ce Wacce Zai Karawa Gashinki Kyau Yayi Haske.


Kasami shinkafar ki kopi ko dai yadda Yakama sai ki jikata da ruwa kibar shi sai yakai minti 30 zuwa 40 .


Kinga yayi kamar Madara Madara daganan saiki tsiyaye ruwan ki wanke kanki dashi.


Daganan sai ki kunshe kan Naki da ledarnan da kuke daure Kai kibarshi har zuwa minti 50 ko 60 kana ki wanke da ruwan dumi sai ki tace kan da kum sai Kinga duk dattin shinkafar ta fice.


To shikenan bazi karaba sai bayan kwana 7,haka zirinka yi sati sati to insha Allah saidai kanki ya zama abin tanbaya ga Mata

Post a Comment

Previous Post Next Post