Yadda Ake Saduwa Da Macce Kuma Ba Zatayi Ciki Ba

Yadda Ake Saduwa Da Macce Kuma Ba Zatayi Ciki BaAzalu, shine fitar da azzakari cikin farjin mace a lokacin da namiji yazo yin zuwan kai. Wannan tsarin ne tarihi ya nuna sahabbai na lokacin Manzon Allah (SAW) suna yi domin gudun yiwa matansu ciki. Shine kuma tsarin da Malamai gaba daya suka amince dashi domin hana yiwa mace ciki.

Sai dai kuma wannan tsarin ko a wancan lokacin baya hana shigar ciki haka nan kuma a yanzu.

Ana samun rashin jutuwa lokuta da dama tsakanin ma'auratan da suke yin wannan tsarin na Azalu amma kuma sai suga matan tayi ciki. Ana samun mazan da suke nunawa sam wannan cikin ba nasu bane da hujjar cewa sufa a waje suke zubda maniyi ba a cikin mace ba. Har saki ana samu saboda wannan matsalar bayan a zahiri shi wannan tsari kashi 30 ne kacal cikin 100 na kaucewa hadarin hana yiwa mace ciki.


Wannan yasa masana suka baiwa ma'aurata shawaran cewa kada su dogara da azalu kadai a tsarin hana yiwa mace ciki dole sai sun hada da yin allurai da sauran wasu kariya.

Haka nan muddin namiji na son yin amfani da wannan tsarin na azalu dole ne ya tabbatar da kamin ya soma yin Jima'i da matarsa ya bari sai tayi masa wasa sosai yadda maziyi ya fito masa sai ya samu damar yin fitsari domin kauda duk wani maniyin dake daf da fitowa kamin nan ya shiga matarsa.


Yin amfani da azalu zai fi tasiri ne a lokacin da matarka bata lokacin kenkensar ta wato ovulation period. Domin abunda akasarin maza basu fahimta ba shine, ba sai namiji yayi zuwan kai bane maniyi yake fitowa daga gabansa ba. A lokacinda namiji yake Jima'i da matarsa ana iya samun maniyi ya yi wuf ya fada mahaifar mace tun ma kamin namiji yayi zuwan kai, don haka ne koda yayi zuwan kan a waje tuni an samu wasu miliyoyin maniyin da suka shiga mahaifar mace kamin mijin nata yayi zuwan kai na gaba daya, da hakan ne kuma zata samu damar yin ciki sai namiji yazo yana cewa ba shi ne yayi cikin ba.

Hanya mafi sauki muddin namiji yana son yin azalu to ya tabbatar akwai wasu hanyoyin da zai kara dasu amma ba shi kadai ba domin azalu bai hana shigan ciki.


Da fatan maza ma'aurata sun fahimci karatun.

Post a Comment

Previous Post Next Post