Rashin Sha'awa Ga Matar Aure, Da Kuma Yadda Za a Magance Matsalar

 Rashin Sha'awa Ga Matar Aure, Da Kuma Yadda Za a Magance Matsalar


TAMBAYA

Malam Dan Allah mene magnin rashin sha awa gamacen aure kuma menene yake kawota Allah yakarawa malam lpa da ilimi mai amfani_

MSA

_Toh dai ita sha'awa Bata da tasiri ga Wanda yake da damuwa ko Rashin kwanciyar hankali da Kuma Rashin Jin dadin Zaman da miji._

Abinda Ke Kawo Kukan Dadi Yayin Saduwa Da Matar Aure 


_Sanan Kuma akwai Wanda halittarsu Haka Allah ya haliccesu Basu da qarfin sha'awa domin akwai banbancin sha'awa kafin aure da Kuma sha'awa Bayan aure anan ake banbance Mai qarfin sha'awa da Mai saukin sha'awa domin zakiga wani kafin aure Kamar zaici babu Amma ana Gama cin amarci sai kiga sha'awa tayi laqwas wani Kuma sanann Zaki ga Sabuwar sha'awa ta bayyana gareshi shiyasa ba'a hukunci da sha'awa sai mutum yayi aure Kuma anga yadda sha'awarsa ta kasance._

_Sannan ga Mata amare bazasu iya tantance sha'awasu da gamsuwar aure ba sai sun dan Jima agidan miji domin na farko Jin zafi da fargabar saduwa na hanasu Sha'awa, ni'ima da kuma gamsuwa akan hakane ma Zaki ga mace na jin sha'awa Amma mijinta na zuwa kanta sai sha'awa ta dauke ta nemeta ta rasa sabida ba yadda za'ayi asamu Biyan buqata mutuqar ba nutsuwa , shauqi da karkashi a wajen ibada aure._

_Sanan Kuma dadin dawa ciwon sanyi na taka rawa wajen dakushe sha'awa da gamsuwa._

_Sanann qiyayya ga Miji ko Jin haushinsa daliin wani Abu da yayi mace ya taba Mata zuciya Duk suna hana sha'awa tasiri._

_Ita fa sadurwa auren Bata da tasiri mutuqar tsakanin Mata da miji Basu samu karkashiba da son abin alokacin da zai faru Amma mutuqar wani bashi da annashuwa toh dadin zai zama ragagge sai dai ayi Dan Biyan buqata Amma ba dandana zaqin jima'iba._

_Amma ga Dan wani Hadi zai iya taimakawa wajen motsa sha'awa ga mace ko namiji Amma shima bazai tasiri ba muqar da abinda na bayyana a sama.._

_Asamu: yansun , garin Ruman, cittta, kanimfari Na'a na'a ko wanne cokkali Daya sai a dakesu su Zama Gari sai ki samu Zuma Mai kyau Mara Hadi sai ki Zuba a ciki ki dafa kamar minti 10 a garwashi Amma kada ya qone, Zaki dinga Sha Babban cokali 1 safe da yamma sati 2 zakiyi, ko Kuma adinga dibar teaspoon asa a kofi sai azuba tafasasshen ruwan zafi akansa abashi mint 15 sai asa Zuma cokali 1 Asha sau 2 arana insha Allah wanan zai sa sha'awa da samun nutsawa da sa annashuwa ga ma'aura yayin ibadar aure._

```Allah ta'ala yasa mudace```

Post a Comment

Previous Post Next Post