Yadda Ake Yin Man Ja Da Kuma Amfanin Man Ja A Jikin Mutum.

Yadda Ake Yin Man Ja Da Kuma Amfanin Man Ja A Jikin Mutum. 



   Yadda za ka haÉ—a Man jan da za ka yi amfani da shi a gida cikin sauÆ™i da tsafta ga kuma samun ingantaccen Man ja wanda ba gauraye. 

    A Æ™arshe kuma za mu kawo muku yadda Man ja ke inganta lafiyar mutane.

    Yadda ake yin Man ja.

   1- Da fari a samu kwakwar Man ja mai kyau, mai tsoka ake zaÉ“a, sai a wanke ta, a cire datti, a gyarata.

   2- A dafa kwakwar Man ja tsawon kamar awa uku ko kuma har lokacin da ta yi taushi sosai.

     3- A zuba kwakwar Man jan a tirmi, a kirÉ“a ta ko kuma a mitstsiketa, har sai an cire tsokar daga jikin Æ™wallayen gaba É—aya, sai a ware su daban.

     4- A mayar da tsokar kwakwar Man jan kan wuta, a cigaba da dafawa har sai man ya fito sosai. 


Karanta Wannan: Rashin Sha'awa Ga Matan Aure, Domin Magancewa A Karanta Da Kyau

      5- A samu mataci a tace Manjan a raba shi da harzar kwakwar.

       Shi kenan Man ja ya samu.

     Amfanin Man Ja Wajen Ƙara Lafiya.

Man ja, wanda ake samar da shi daga jikin Æ´aÆ´an kwakwar Man ja, an É—auki É—aruruwan shekaru ana amfani da shi kuma ya zama É—aya daga cikin mayukan da aka fi amfani da su a duk duniya. 

  

      Ga Wasu Daga Cikin Amfaninsa. 

1. Cutar Kansa (cancer) da cututtukan da ke kama zuciya. 

      Man ja cike ya ke da sinadarin 'vitamin E' wato sinadarin nan da ke gina garkuwar jiki da rage haÉ—arin kamuwa da cututtukan zuciya da kuma cutar kansa idan aka same wadataccensa acikin jiki. To Manja yana É—auke da shi da yawa.

2. Samar da ingantacciyar lafiya ga Æ™waÆ™walwa. 

      'Tocotrienol' da ake samu acikin Man ja yana da alaka kai tsaye da samarwa Æ™waÆ™walwa ingantacciyar lafiya tare da kare Æ™waÆ™walwa daga wasu cututtuka da kan iya shafarta. 

3. Lafiyar tsokar zuciya. 

      Bincike ya nuna cewa 'vitamin E' da ke cikin Man ja na Æ™arawa zuciya lafiya sannan yana rage ko kuma magance cututtukan zuciya ga wasu marasa lafiyar. Ingantaccen Man ja mara garwaye zai iya zama babban taimako ga masu fama da ciwukan zuciya. 

4. Ƙara Ƙarfin Ido. 

     Man ja na Æ™ara Æ™arfin ido saboda 'vitamin A' da ake samu acikinsa wanda ke Æ™ara lafiya da kuma kula da idanu wajen Æ™ara Æ™arfin gani. 

   Idan kuna bukatar sanin amfanin ni wani abinci ko magani ko yadda ake sarrafa wani magani sai ku yi magana ta wajen comment, za mu kawo muku insha Allahu.

    Daga shafin Bashir Halilu.

Post a Comment

0 Comments