Shin Matsayinki Na Cikakkiyar Macce Kin Taba Sirri Da Ƴaƴan Magarya???

 Shin Matsayinki Na Cikakkiyar Macce Kin Taba Sirri Da Ƴaƴan Magarya??? Itaciyar magarya wadda aka fi sani da (Assidir) a larabce kuma (Lote) a turance, itaciya ce mai albarka da dadewa Annabi (SAWW) ya tabbatar da amfaninta.

Magarya na kunshe da magunguna masu matukar mahimmanci ga jikin dan Adam kuma ta na da karfin kashe kwayoyin cuta cikin dan kankanin lokaci.

Ita Magarya Antibiotic ce mai karfin gaske kuma cikin ikon Allah ba ta da wani illa wato side effects na a zo a gani.

Magarya, wadda ƙananan ƴaƴan itaciya ce, ana samunsu a ko'ina a sassan duniya. 

Waɗannan ƴaƴan itaciyar ba kawai tushen ƴaƴan itatuwa ba ce, amma kuma su na da kaddarorin sinadarin magani a tattare da su. 

Tare da ɗanɗano mai daɗi, mutane kan yi amfani da Magarya bayan an busar da ita. 

Haka nan, bayan ƴaƴan itaciyar ana amfani da ganyen domin magunganu daban-daban. 

An san Magarya da sinadarin "antioxidant" kuma ta na iya taimakawa wajen magance damuwa da rashin barci, ta na kuma taimakawa wajen narkar da abinci cikin sauƙi. 

Har ila yau, ƴaƴan itaciyar ta ƙunshi nau'in alkaloids, da saponin, da kuma triterpenoid. Dukkan sinadaran uku su na taimakawa wajen tsaftace jini. Kyakkyawan tsaftataccen jini alama ce da ke nuna cewa duk mahimman gaɓoɓi sun sami isashshen jini mai wadatar iskar oxygen. Wannan ya na sanya ƙara samun kuzari da ingantacciyar lafiya.

Akwai nau'in bitamin C a cikin Magarya, wadda ya ke fitar da fata mara kyau da kuma bayar da kariya ga fatar domin lafiyayya ta samu gurbin zama.

Bugu da ƙari, Magarya na da amfani ga tsarin juyawar ƙwaƙwalwa. A al'adance wasu mata kan yi amfani da Magarya domin rage juyayi da damuwa. 

An bayyana cewa, Magarya na taimakwa wajen rage ƙiba, kuma ta na zama rigakafi ga kamuwa ga wasu ƙananan cututtuka. 

Wane bincike ya kuma nuna cewar, Magarya za ta iya zama babban tushen sinadarin "calcium da phosphorous," wadda ke taimakawa wajen kula da ƙarkon ƙashin jikin ɗan adam. Musamman ga tsofaffi ko mutaonen da ke da raunin ƙashi.

Post a Comment

Previous Post Next Post