Muhimmancin Shan Kunun Aya A Jikin Dan Adam

Muhimmancin Shan Kunun Aya A Jikin Dan Adam Aya wacce muka sani a kasar Hausa,ana kiranta da tigernut a harshen Turanci,Yarubawa na kiranta da suna Ofio,a yayinda su kuma Kabilar Igbo suke kiranta da suna imumu ko aki.


Ana samun aya a sassa daban daban a kasashen duniya ciki harda Nigeria.


A can baya,an dauki aya tamkar kayan kwalamane kawai wanda yara ke ci dan jin zaqi ga bakinsu wanda yasa har daquwar ayar ake yi ana siyarwa.wannan baya rasa nasaba da rashin samun cikakken bayanin alfanon aya.Daga bisani sai kimiyya ta bankado binciken wasu masana akan dimbin amfanin aya wanda jin haka yasa har kunun aya ake yi a yanzu.


Sai dai kuma har zuwa yanzu akoi mutane da dama da basu san amfanin shan kunun aya ba,inda wasu sun dauka abinsha ne kawai maganin yunwa ko kayan marmari.wasu ma kayan zaqi suka dauke shi.


Ganin haka,yasa na zo maku da bayani tiryan tiryan kan aya da kuma amfaninta.


Aya tana kumshe da wasu muhimman sinadirrai na musamman dake gina jiki,masu inganta lafiyar jinin jiki da tsokar gangar jikin dan adam,masu kare jiki daga kamuwa da wasu kwayoyin cuta,masu maganin wasu illoli da matsalolin dake damun maza da mata da makamantansu.


Kadan daga cikin wadannan sinadiran sun hada da : Phosphorus,vit E,Fat,protein,dietry fibre,potassium,zinc,sodium,calcium,magnesium,copper,vit C, da carbohydrates.


Anyi amanna cewa aya tana sanya jini kaiwa da kawowa a cikin kowane lungu nda sako na jiyojin jiki (proper circulation) wanda a dalilin haka yasa ake ganin tana karin shawa da karfin zakari ga namiji domin jiyojin zakari zasu rinka samun jini wadatacce da zai rinka kaiwa da kawowa.


Aya tana samarwa jiki da wadataccen sinadirin Vitamin E da vitamin C da kuma Zinc da sinadirin quercetin wanda suke da matukar amfani ga mace ko namiji musamman masu neman haihuwa.


Aya tana kara yawan ruwan maniyi da kuma lafiyarsa (quantity and quality sperm count) ga namijin da ruwan maniyinsa suka ja baya ko yake fama da karamcin 'ya'yan maniyi a jiki(low sperm count)


Aya tana karawa mata ni'ima-sai a nemi ayar misalin gongonin madara daya da kuma garin dabino rabin gongoni sai a hada da ciyarwa nan da ake kira dan hakin daka raina sai a dake a maidata daquwa ko a maidasu tamkar alawa a zanka ci.kada a saka suga ko kadan.


Aya tana kara yawan ruwan maniyi ga namiji sai a nemi garin aya gongoni daya sai a sanya ruwan kwakwa a dame garin a zanka sha.


Aya na samarda yawan oestrogen wanda karamcinsa na haifarda rashin haihuwa ga mata.


Aya na samarda testosterone wanda shi ne male sex hormone,inda ya karamta ga jikin namiji to zai kasance baya da shawa tamkar bai balaga ba,zai ga yana ramewa kuma zakarinsa baya karuwa haka kuma zai kasance baya da maniyi lafiyayye wanda wannan zai hana shi haihuwa.


Masu fama da wannan matsalar sai su tuntu6eni wannan hadin yana bukatar bayani na daban.


Aya tana samarda sinadiran Vit E ga jiki wadanda ke kara yawaitar maniyi da kuma lafiyar sa.


Wadnda ke taimakawa mata samun damar nasa qwai (ovulation) wanda rashin yin ovulating ko rashin nasa qwai ga mace zai hanata daukan juna biyu.Wannan dalilin ne yasa ai matan da suka tsufa basa daukan juna biyu domin sun daina nasa kwai.


Mata da kuma mazan da suke da qalubale na rashin samun haihuwa sai su rinka amfani da aya akai akai.


Amma fa a kaucewa amfani da suga,wannna natural drink ne akoi suga ta daban a ciki da bata bukatar wata suga can ta daban.


Aya na kara yawan ruwan nono.Dan haka ga duk macen dake shayarwa sai ta rinka amfani da kunun aya akai akai bayan taci abinci.


Mazan dake neman amfanuwa da aya sai a zanka hada garinta dana citta a nike sai sun koma gari sai a sanya babban cokali biyu a cikin zuma a sha.


Idan anci abinci to sai a nemi cup daya na kunun aya a sha.hakan zai taimakawa ciki dan saurin narkarda abinci.


Idan aka hada garin tafarnuwa dana citta da garin aya aka dama a tare da zuma zai bada wasu magungunnan na daban wadanda za muyi bayaninsu nan zuwa gaba. 


Mai fama da bayan gari mai tauri kamarna dabbobi to sai ya rage cin shinkafa da abinci mai karfi sai ya zanka shan diyan itatuwa daga bisani yabiyo baya da shan kunun aya.

Kada a hada kunun aya da madara wanda hakan zai sa concentration din yayi yawa.yana ma iya zama wani abu na daban da baidace da lafiya ba.

Kada a sanya suga. 

Kada a tafasa 

za a iya hada kwakwa ko dabino a madadin suga.

Post a Comment

Previous Post Next Post