Abinda Ke Kawo Fitar Budurci Da Yadda Za a Dawo Dashi

 Abinda Ke Kawo Fitar Budurci Da Yadda Za a Dawo Dashi 




Dazu na ce idan na samu lokaci zamuyi magana sosai akai, to gudun kada Abubuwa suyi yawa nace bara nai magana yanzu. Saboda yanzu muna wanu lokaci da yakamata a Kara Jan hankalin Mata da Kuma iyaye akan Abubuwanda ke faruwa na yawaitar yiwa Mata ciki ko Fyade. Amma inshaAllahu zamu danyi bayani yanzu ko kadanne.


A hitta Allah ya halicci gaban mace da siffofi daban daban tundaga waje Inda ake iya gani da ido har zuwa ciki (Mahaifa kenan). Kuma suna taka rawa sosai a rayuwar kowacce mace, Daga waje Ana iya ganin gaban mace kofa daya zuwa biyu, wadda daya a sama daya kasa. A Hausa ake cewa wajan fitsari da wajen Kashi.


To wajan fitsarin shima akwai kofofi Daga ciki, wadda anan ake samun Mahaifa, da kuma kofar da ake yin fitsarin, bayan wadannan akwai kananan kofofi wadda Allah ya halitta wadanda suke fitarda Gumi da kuma majina domin taimakawa Gaban mace wajan daidaita Lafiyarsa da kuma inganta tsaronsa. Kofofi guda biyu da muka ambata a gaban mace daya a Sama, daya a kasa. Ta saman ta ita ake fitsari, ta kuma itace wadda zamuyi magana akai wadda tanan dukkan mace take haihuwa kuma tanan ne ake saduwa da mace.


Ita wannan kofa Allah ya sanya mata wani murfi da ake kira (Hymen) da turanci wasu kuma suce BUDURCI da Hausa kenan, kuma shi wannan budurci kusan kala hudu ne.

Karanta Wannan: Yadda Ake Matsin Ciki Da Wajen Macce Hadin Tafarnuwa 

1. Akwai mai laushi.

2. Akwai mai Raga_Raga Amma yanada kauri Fatarshi.

3. Akwai Wanda tsoka ne amma da 'yar Huda Kadan.

4. Akwai kuma Wanda a like yake sosai Wanda sai an tsagashi kafin a cireshi.


Zamu iya cewa wannan wata Daraja Allah (T) ke nunawa a gareki yasa kika samu wadannan matakai na tsaro domin ya nuna muhimmancinki da Muhimmancin wannan gun a tare dake, domin ko babu komai Duniya ta taru ne ta wannan guri kuma tana kara cigaba ta wannan guri.


Abubuwa da dama na sanyawa wannan Murfin ya lalace amma ba kowanne irin Murfin ke lalaceea ba. Akwai Hanyoyi kanana Wanda zai iya lalacewa amma kuma bazai zama kofar ta bude ba, akwai kuma manyan Hanyoyi sanannu Wanda indai akai anfani dasu Zai lalace kuma hanyar ta bude.


Hanyoyin Farko :


Yawan Motsa Jiki 

Yawan Daukar Abu mai nauyi.

Hawa keke

Dadai abubuwa wadanda zasu iya sanyawa ki bude kafafunki sosai.


Hanyoyi na Biyu kuwa :


Sex (Saduwa), Tunda ta wannan hanyar namiji ke saduwa da mace, indai ya shigeta to dolene wannan Murfin ya futa.


Wasa da gun kamar sanya yatsa da wasu sukeyi yayin jin sha'awa, ko kuma sanya wani Abu da zai iya Fasa wannan Murfin ya shiga kofar.


Indai mace tanada kiyayewa wannan murfin bazai samu matsala ba duk shekarunda zata dauka kuwa a gida batai aureba, kuma matsi daban Hymen daban.


Jini da ake cewa ana gani idan ankusanci mace ba shike nuna lallai ita budurwa bace, yana iya zama haka. Amma idan mace a matse take idan za'a sadu da ita ana iya ganin jini koda kuwa tanada shekaru da dama.


Kiyaye wannan kofar shi ne Abu mafi daraja a rayuwarki a matsayinki na mace, domin kuwa darajar mace da ake fada tana nan ne kuma burin iyaye kenan su kiyaye wannan darajar, idan kikai sake kika rasata to duk wani Jan aji da kike a matsayinki na mace ya Kare.


Danhaka saimu kula mu kiyaye domin mutuncin Iyayenmu da zuri'armu Baki daya, da kuma mutunta addininmu.


Budurcinki 'Yancinki.


GA WANDA SUKA RASASHI TA HANYAR TSAUTSAYI NA FYADE KO WASU ABUBUWA WANDA BAA RASA BA Zamu Bada Taimako 

Sosai daza kikoma daidai Yar uwa Koda kuwa kin haihu kinaso kikara matsewa kubiyomu


1 Comments

Post a Comment

Previous Post Next Post