Jamar unguwar su, da manyan malaman garin da take zaune sun yi mata karatun ta nutsu domin ganin ta daina wannan shashanci da ta dake da sunan sana'a wato wake-wake da raye-raye.
Mutane da yawa suna yawan tambayar shin ko dai Safara'u Kwana Chasa'een ba ta da mahaifa ne? To amma abin da suka manta da shi shi ne, ita shiriya ta Allah ce ya kan shirya wanda ya so ne kuma a lokacin da ya so. Ko da mahaifanka na raye idan rabbil sama wati bai nufe ka da shiriya ba sai ka rayu kamar matacce.
Idan dai kai cikakken masoyi Manzon Allah ne abu mafi kyau da zaka yi akan wannan yarinyar Safara'u shi ne addu'a Allah ya shiryata ta gane abin da take yi ba kyau ta daina.
0 Comments