Hanyoyi Mafi Inganci Da Ake Samun Kudi A Kafafen Sadarwa (Internet)

 Hanyoyi Mafi Inganci Da Zakabi Ka Samu Kuɗi A Internet.

Da akwai hanyoyin da yawa na samun kuɗi a kafar sadarwa, to amma kasancewar akwai mayaudara sun yi yawa sosai a kafar sadarwa (Internet) ya sa mutane da yawa basa yarda da hanyoyin. Hakan ne yasa ArewacinNaija News mu ka yi nazarin kawo muku hanyoyi Mafi inganci da zaku samu kuɗi. Kamar yadda kuka sani duk aikin da za ayi a samu halak tana da wahala amma idan mutun ya kasance mai dauriya to zai samu halak dinsa cikin sauki. Kamar yadda ma'aikatan labura, wasu kuma aikin gwamnati wasu yan kasuwa ke yi su samu kudi haka wadan nan hanyoyin suke. Wasu hanyoyin kudi ake zubawa ma'ana hannun jari sai a samu kudi halak a dan wani lokaci wasu hanyoyin kuma aiki ake yi a biya mutun kamar yadda ma'aikatan gwamnati ke yi a biya su a kowane wata ko mako.


Hanyoyi Mafi Sauki Wurin Samun Kudi Su ne:


Affiliate Marketing; Ma'anar Affiliate Marketing shi ne kulla hulda a tsakaninka da wasu kamfunan sadarwa wanda zasu baka tallar wasu goods and services na su kana yi musu talla kana kawo musu customers suna siyan kayansu. Ita wannan hanya tana da matukar sauki sosai domin kuwa babu yaudara a cikinta kawai idan aka bi dokokinta za'a samu abinda ake so. 

Social Media Handling: Ma'anar Social Media Handling shi ne kula da wani shafin yan kasuwa ko kuma wasu wadanda basa da lokacin kulawa da shafinsu. Irin wannan yafi kasancewa a wurin wadanda basa da wadataccen lokacin kansu kamar yan kwallo ko kuma mawaka ko dai wasu manyan celebrities zasu baka handle nasu kana kula musu da shi zasu na biyan ka kuɗin aikin da kake musu.

Blogging And Youtubing; Ma'anar Blogging shi ne gina wani shafi wanda ake yi domin tallace-tallace ko kuma yada wasu labarai. Shi kuma Youtubing na nufin kirkira channel domin saka videos a ciki mutane suna kalla ya danganta da irin videon da kake iya yi ko dai gyaran waya ko kuma yada labarai ko kuma magungunan gargajiya ko videon ban dariya ko na Film, duk dai abin da ka ji zaka iya yi. Idan ka iya hada videos ko labari naka na kanka ba na wani ba kuma ka bi dukan dokokin to kamfanin Google da kansu ne zasu na biyan ka wasu kudade masu tsoka.

Influencing/Public figure; Ita ma wannan hanyar amintacciyar hanya ce wacce ake bi domin samun kudi. Ma'anar influencing Public figure shi ne samun followers da yawa a shafinka, wanda idan ka samu followers da yawa a shafinka na Instagram ko kuma telegram ko kuma twitter ko facebook koma wane shafi ne. Kamfani da yawa za su baka tallar kayansu wasu ma har ambassador za su baka wanda zasu na biyan ka albashi mai tsoka a kowane wata, kamar yadda kuke ganin manyan celebrities na yi wasu na tallar MacLean wasu na tallar tufafi wasu motoci wasu kuma kayan abinci wasu kuma magunguna wasu kuma kamfuna suke talla.

Kana da babbar waya wacce takai kimanin kudi Naira dubu talatin ko fiye amma baka neman kudi a kafafen sadarwa to idan wayar ta fashe fa sai ka cire wasu kudaden ka yi gyara haka zaka cigaba da yi wa wayarka bauta tamkar wata matarka. Yakamata kana neman kudi da ita. Ka yi kokarin jarraba wata hanya daga cikin wadan nan hanyoyin.

Post a Comment

Previous Post Next Post