Shin Sperm Na Iya Rayuwa Kwanaki Nawa a Jikin Mace?
Tambayar tsawon lokacin da maniyyi (sperm) ke rayuwa a jikin mace tana da muhimmanci sosai, musamman wajen fahimtar yadda daukar ciki ke faruwa.
A cewar masana kiwon lafiya sperm na iya rayuwa har zuwa kwanaki 3 zuwa 5 a cikin jikin mace, idan yanayin ya dace.
Yaya Sperm Ke Rayuwa a Jikin Mace?
~~~~~~~~~
Bayan jima’i, maniyyi na shiga cikin mahaifa ta bakin mahaifa (cervix), sannan ya wuce zuwa mahaifa da bututun fallopian tubes.
Idan yanayin jikin mace yana da kyau (musamman lokacin ovulation), sperm na iya:
– rayuwa har kwanaki 5
– jira kwai ya fito domin haduwa da shi
Amma idan yanayin bai dace ba, sperm na iya mutuwa cikin awanni kaÉ—an zuwa rana 1.
Me Ke Taimakawa Sperm Rayuwa Tsawon Lokaci?
~~~~~~~
1. Lokacin Ovulation
Lokacin da mace ke kusa da fitar kwai (ovulation), akwai ruwa a bakin mahaifa da ake kira cervical mucus wanda:
– ke kare sperm
– ke taimaka masa motsi cikin sauÆ™i
Wannan na ba sperm damar rayuwa har kwanaki 5.
2. Yanayin Jikin Mace (pH Balance)
Idan yanayin farji ya yi daidai (ba mai tsananin acid ba):
– sperm na rayuwa tsawon lokaci
– idan ya yi acidic sosai, sperm na mutuwa da wuri
3. Ingancin Maniyyi
Sperm mai ƙarfi da lafiya:
– na rayuwa fiye da wanda bai da Æ™arfi
– na iya kaiwa ga kwai cikin sauÆ™i
Shin Ana Iya Daukar Ciki Bayan Kwanaki?
~~~~~~~
Eh. Wannan shi ne abin da ke rikitar da mutane.
Saboda sperm na iya rayuwa har kwanaki 5:
👉 mace na iya daukar ciki ko da an yi jima’i kwanaki 3–5 kafin ovulation.
Wato:
– ba sai ranar ovulation aka yi jima’i ba
– sperm na iya jira kwai ya fito
Abin da Yake Kashe Sperm da Wuri
~~~~~~~~~~
– yanayin acid mai yawa a farji
– rashin ruwa (dryness)
– zafi ko yanayi mara kyau
– amfani da wasu sinadarai (misali sabulu masu karfi)
Lafiya Uwar Jiki


0 Comments