Cikakken Bayani Akan Mutumin Da Akewa Zargin Ma'ilaka Ne A Saudiya

Cikakken Bayani Akan Mutumin Da Akewa Zargin Ma'ilaka Ne A Saudiya  Allah Sarki na jima da sani labaran wadanan mutanen .. 

Su duka da kuke ganin hotansu .. sun kasan ce (kinnar) ne ko kace hermaphrodites ta hausa kace mata maza .. 

Har wanan malamin da kuke gani asalin sa da mace ne ya koma namiji .

Musamma a India indai aka ce Kai mata maza ne to ka shiga uku ka ringa samun tsana da tsangwama da bakin ciki a rayuwa, shiyasa ma aka ware musu community dinsu daban ..

Yawancin su sana'ar rawa suke yi wasu Kuma bara suke yi akan titi .. anan ne kafin kaga mata maza abin da wuya Amma a India haka zaga gansu akan titi suna bara ..

Kai na takaice maka a community dinsu na hermaphrodites wato mata maza idan Daya ya mutu daga cikinsu to biki suka yi suna murna wai Yar uwarsu ko Dan uwansu ya bar bakin cikin Duniya. Suna rayuwa cikin kunci ne ..

Shi wanan malamin da kuke gani da Shima mace ne Sai Allah ya nuna masa hanyar gaskiya ya karbi addinin musulunci yayi Kuma karatun addini sosai , shine yake bi Yana musuluntar da Yan uwansa Yana nuna musu hanyar gaskiya..

Shi wanan Wanda wasu ke cewa ko ma'ika ne wanan malamin ne ya shiryar da shi ya karbi addinin musulunci lokacin da ya karbi addinin musulunci har ya je makka umara video da ake yadawa ya jima Bai wai na yanzu bane..

DUK acikinsu wanan malamin ne yake ruko da addini sosoi Amma zaka biyun har yanzu Basu daina wanan sana'ar ta su ta rawa ba . Amma lailai wanan malamin Yana iya bakin kokarinsa wajan nuna musu hanyar gaskiya.

Post a Comment

Previous Post Next Post