Matsalar Warin Baki Ga Wasu Mutanen Maza Da Mata

Matsalar Warin Baki Ga Wasu Mutanen Maza Da Mata



Warin baki shi ne lokacin da mutum ya ke magana sai wari ko É—oyi mara daÉ—i ya dinga fita daga bakinsa, wani ma ko bai yi magana ba numfashinsa ma kawai wari ya ke fitarwa. Wani idan yana da warin baki shi kansa yana jin warin, wani kuma ba ya ji, sai dai kawai ya ga in yana magana mutane suna toshe hanci ko kau da fuska. 


   Mutum


na iya kamuwa da matsalar warin baki saboda dalilai da dama. Ga wasu daga ciki. 


1- Rashin tsaftar baki. 

    Rashin wanke baki yadda ya kamata na iya sa wa wasu Æ™wayoyin cuta su dinga girma da yawaita acikin bakin mutum, waÉ—anda ke maida abincin da ya maÆ™ale acikin baki ya koma mai wari ko É—oyi. 

Karanta Wannan: Shin Kunsan Amfanin Bawan Albasa ???

     2- Rashin sakace baki idan an ci abinci. 

       Musamman nama ko kifi da dai sauransu, ragowar abincin da ya maÆ™ale acikin haÆ™ora ba a sakace shi ba, yana ruÉ“ewa ne a cikin haÆ™oran, ya dinga É—oyi, wani sa'in ma yana yin tsutsotsi, wanda hakan ke haifar da warin baki da ciwon haÆ™ora. 


     3- Bushewar baki. 

          Idan ya zama miyau na É—aukewa a bakin mutum, zai zama bakinsa yana bushewa, wanda hakan ke sa wasu Æ™wayoyin halitta a bakin mutum su dinga wari. 



   4- Shan taba. 

      Shan taba kan iya janyo warin baki saboda sinadarai masu Æ™arfi da ke cikinta da kuma yadda ta ke ta'adi ga lafiyar bakin mutum. 


       5- Kogon haÆ™ori, olsar baki da kuma rauni acikin baki. 

      Dukkan waÉ—annan suna iya kama abincin da mutum ya ci, su riÆ™eahi a jikinsu, har ya ruÉ“e acikin baki ya dinga wari. 


Hanyoyi Da Wasu Dabarun Yadda Zaka Dade Akan Macce

     6- Cututtukan baki. 

            Kamar cirewar haÆ™ori, ruÉ“ewar haÆ™ori da kuma cututtukan dadashi, duk suna iya janyo warin baki. 


  7- Diabetes da wasu nau'ukan rashin lafiya na iya sa wa bakin mutum ya dinga wari. 


      8- Rashin cin abinci ko yin Azumi. 

        Idan mutum ya É—au lokaci mai tswo bai ci abinci ba hakan na iya sa wa idan yay numfashi a dinga jin wari yana fita daga bakinsa saboda babu komai a cikinsa, sai abinda ya daÉ—e acikin hanji.


    9- Cin abinci mai É—auke da acid da yawa. 

     Kamar Albasa, tafarnuwa, da dai sauransu. WaÉ—annan kan sa warin acid É—in ya dinga tasowa idan mutum yana maga, suna fitowa ta bakinsa.



    Da akwai hanyoyi da dama da ake bi domin magance warin baki da kuma hnayoyin rigakafi.

Post a Comment

0 Comments