Tsaftar Macce Da Namiji Akan Saduwa A Lokacin Sanyi

 Tsaftar Macce Da Namiji Akan Saduwa A Lokacin Sanyi 1.Shaving cream: Wannan man kala-kala ne sai wanda ka za’ba amma wanda mutane suka fi sani ko suka fi amfani da shi shine veet. Idan mutum ya je toilet sai ya shafa cream a in da gashi suka fito masa ya bashi minti 5, akwai abun da ya ke zuwa a ciki na roba shi za a fara cire mai da gashin, sannan za a iya sake sharewa da tissue kafin a zuba ruwa a wanke, kin ga babu wani abun cutarwa da zai shiga cikin farjinki. Shaving cream amfanin sa na da yawa bayan ya cire gashi zai bada gudunmuwar daďewa gashi bai fito ba, ba kamar amfani da shaving stick ba. Sannan shaving cream bayi da wari kamar yanda na ji wasu mata na ta surutai a kai, wata ma kila bata ta’ba amfani da shi ba labari ta ji kawai, don haka bayi da wari kamar yanda ake faďi.

Karanta Wannan: Gyaran Lebe A Lokacin Sanyi

2.Shaving Power: Shi ma ďin kala-kala ne amma yawanci maza sun fi amfani da shaving powder, shi gaskiya yana da wari sosai shi yasa mutane ke gudunsa, kuma yana da karfi sosai, domin idan ya daďe a jikin mutum zai iya farfasa masa fata. Fari ne kamar powder, idan za a yi amfani da shi sai a debi dai-dai yanda zai isa a ďan sa masa ruwa sannan a shafa.


3.Shaving razor stick: Ga mace ana so ta kiyaye sa wannan cream din ko powder a dai-dai wurin farjinta, saboda guje ma cutarwa wa, a sama zaki sa qasan kuma sai ki yi amfani da shaving stick ki cire ragowar. Sannan shi shaving stick ana ajiye shine saboda ran da baka jin sa cream sai a yi amfani da shi, kuma is safer akan ki yi amfani da reza. Duka wadannan a shago daya za a same su a kasuwa, man cire gashi da rezan aski.


4.Zaitun: Mutane da yawa idan sun yi shaving haka suke barin wurin to ba a haka, duk lokacin da mutum yayi shaving ya wanke wurin, kafin ya fito ko bayan ya fito toilet sai ya shafa zaitun sosai a wuraren nan guda biyu, tabbas mutum zai sami jin dadi a jikin sa ma, musamman mace domin wani zai iya sawa ki ji ki a bushe ko qaiqayi.


Gaskiya qazanta ya kai qazanta a ce namiji ko mace basa rage gashin jikin su, saboda al’aura wuri ne da ya ke fitar da abubuwa da yawa musamman ga mace, idan kika ce ba zaki tsaftace wurin ki gyara shi ba, to dukkan kazantar da kika fitar shi ma zai nemi wuri ne ya zauna, duk wannan jinin zai maqale ke kin ďauka kin wanke amma kuma ya nemi wuri a cikin gashin ya zauna, sannan ba za’a raba ki da kuraje, wari da soshe-soshe ba tun da dai kin bar wurin ba tsafta. Sannan babu aji ga mace ko namiji su ďaga hammata a ga gashi dunguzun duk datti, don haka yana da kyau a rinka yanke gashi a kai a kai a yi koyi da Annabi.

Post a Comment

Previous Post Next Post