Sabon Hadin Agwaluma Domin Mata

Sabon Hadin Agwaluma Domin Mata


Tabbass lafiya ita ce uwarjiki kuma kowa ya kwana lafiya shine ya so hakan. 

Akwai wasu tarin yayan itatuwa da ke da tarin alfanu sannan kuma basu da wata illa ga jikin dan Adam.

 sai dai mutane da dama basu san don haka ba hakan ne yasa muka lalubo maku wasu daga cikin amfanin agwaluma.

 Wani sabon binciken kimiyya ya nuna cewa za a iya amfani da ganyayyaki da itacen Agwaluma wajen magance wasu cututtuka a jikin dan adam. 

Amfanin agwaluma 5 a jikin dan Adam Source:

 UGC 1. Agwaluma na maganin zazzabin Malaria mai naci ko wanda bai jin magani.

 Binciken wanda aka wallafa a kundin BMC Complementary and Alternative Medicine ya bayyana cewa wannan magani ka iya zama sabuwar karbabbiyar hanyar magance zazzabin duba da rashin nasarar da ake samu da sauran nau’ikan magunguna.

 2. Agwaluma dai na dauke da sinadarin Vitamin C, wanda ke da matukar amfani a jikin dan adam.

 3. Agwaluma na da matukar amfani ga mai dauke da juna biyu. Shan agwaluma na tsayar da amai da jiri wanda juna biyu ke haifarwa. 

4. Sannan idan mutum baya so yayi kiba day a wuce misali sannan yana bukatar sinadarin gyaran idanu da zuciya toh agwaluma na taimakawa sosai wajen cimma hakan.

 5. Yana kuma taimakawa wajen samun bacci cikin kwanciyar hankali. Sannan kuma yana rage ciwon gabbobin jiki

Post a Comment

Previous Post Next Post