Shawarwari Zuwa Ga Amare Daga Bakin Mallama Juwairiyya Bintu Usman

Shawarwari Zuwa Ga Amare Daga Bakin Mallama Juwairiyya Bintu Usman 


Danna Hoton Ko Download Domin Kallon Bidiyon Ko Saukewa 

1. Tundaga farko amarya tsarkake zuciya ya kamata kiyi kisa a zuciyar ki cewa aure zakiyi kuma bautar Ubangiji zaki je, musamman idan mai mata zaki aura ki nufe ta da zuciya mai kyau.

Ki saka a zuciyar ki don Allah zaku zauna da wanda kika samu,idan ke kadai ce ma duk daya ne.

2. Amma kina iya shan ‘ya’yan itatuwa da yawa gab da bikin naki, inda hali ma, kina iya daina cin duk wani abinci illa ‘ya’yan itatuwa da ganyayyaki kadai kamar ana sauran sati daya bikin naki.

3. Haka ma magungunan Musulunci da ka samu ingancin warakarsu daga Manzon Allah SAW, irin su zuma, habbatus sauda, zaitun da sauransu. Wadannan za su warkar miki da duk wani rauni ko cikas da kila kina da shi a lafiyar jikinki da ta ruhinki gaba daya.

4. Sai kuma ki rika yawan shan ruwa, a kalla ki sha kofi takwas na ruwa kullum.

5. Amarya babu ruwan ki dayin wani bleaching saboda b'ata kalan fatarki zakiyi,da yawa amare idan za'a yi auran su wasu bleaching sukeyi wai don suyi haske, sai nake ganin mijin yafi ki sani kalan ki yadda kike (ina maganar da bakar mace ce mai canja halittan Allah) ba'a hanaki gyara ba amma kiyi gyara mai kyau ga mayukan gyaran jiki masu kyau wanda zai gyara miki jikin ki,irin su zaki samu masu kyau kiyi gyaran da duk wanda ya ganki yasan bawai bleaching bane saboda yanzu akwai kalan 'yan gayu akwai kuma kalan bleaching  don haka Amarya sai kiyi kalan gayu.

'

6. Amarya idan kinje kin samu mai mata don Allah ki zauna da ita lafiya kuma ki rike 'ya'yan mijin ki idan kika jawo su jikin ki babu yaron da zai miki rashin kunya saboda zuciya tana son mai kyautata mata.

7.kwalliya da ado da zuba kamshi naki ne domin macen datasan kanta kullum cikin kamshi take a ko ina.

8. Amarya a yayin shagalin bikin ki don Allah karkiyi abinda zaki zubar da albarkan auran ki karkiyi irin rashin kunyar da wasu amaren zamanin nan sukeyi,ko kuma irin shigar fitsara wanda bai dace ba.

9. Amarya ki sani cewa dukkan wata soyayyar da kukayi kafin aure ba soyayyah bace, yanzu ne soyayyah yanzu ne idan zama ya hadaku da juna kowa zai San wanene a tsakanin ku, Yanzu ne zaku fahimci junanku.

10.Amarya karki yarda da zugan wasu kawayen domin akwai wasu kawayen da idan har zakina daukar zugan su tsab zasu iya kashe miki aure, shiyasa ake son mutum tun farko ma yasan wane irin kawaye ya dace yana mu'amala dasu.

11. Amarya karki shiga gidan mijin ki da wata munguwar niyya misali: yana da matarsa sai ki shiga da niyyar ai sai na fitar da ita.kinga tundaga waje tun farkon auran ki kin saka munguwar niyya a zuciyar ki.ki gyara karki saka wannan tunanin a zuciyar ki.

12. Amarya ki zama mai kawaici da kauda kanki a komai ma ba kowane abu bane sai kinyi magana wani abin hakuri ake yi.

13. Sannan ki tsabtace zuciyarki da kyawawan shau’uka da tunani da kyautata zato da fatan alheri. Allah Ya ba ku zaman lafiya tare da sauran dukkan ma’aurata Musulmi, amin.

Post a Comment

Previous Post Next Post