Abubuwan Da Mata Za Su Sha Don Dauwamammiyar Ni’ima!

 Abubuwan Da Mata Za Su Sha Don Dauwamammiyar Ni’ima!Da yawa mata su na yawan kawo korafin daukewar ni’ima a jikinsu, wato bushewar gaba, da daukewar sha’awa yayin jima’I, wanda yawancinsu su kan ce da ba haka su ke ba; lokaci guda su ka ji sun kasance a hakan.

Yawancin mata rashin kula da kai da rashin sanin irin abubuwan da yakamata su dinga ci domin samun dauwamammiyar ni’ima a jikinsu don samun gamsuwar kawunansu da jin dadin mazajen shi ke haifar mu su da.matsalar daukewar ni’ima da kuma daukewar sha’awa.

Wasu kuma su kan kamu da ‘toilet infection’ ne saboda rashin tsaftar bandaki, wasu ba sa taba kula da gyaran bandakinsu, wasu kuma su kan dauka a bandakin hadaka..

Abubuwan da ya kamata mata su dinga ci, domin karuwar ni’imar jikinmu da da jin dadin mazajenmu:-

A na son mace ta dinga cin daya ko biyu daga cikin wadannan abubuwan kullum a rana; a cikinsu akwai abubuwa masu saukin kudi wadanda duk rashin hadi ki ko rashin halin maigida, zai iya siya, kuma wadannan abubuwa su na kara lafiya da kuzari a jikkunan aluUmma kuma garkuwa ne ga kamuwa da wasu cutukan. Haka kuma ya na karawa mata ni”ima da jin dadi wajen mazajensu.

Wadannan ba wasu abubuwa ba ne illa:

.

Kankana, Ayaba ,Gwanda, Goba, Lemo, Tumatir, Rake, Aya, Kwakwa, Dafaffiyar gyada, Zuma, Nono, Madara, Madarar Shanu, Gurji, Dabino, Chukwi, Zogale, Ruman, Inibi, Tuffa, Zaitun.

Misali yau idan ki ka sami jikakkiyar ayarki ki ka ci, gobe ki sami raken ki ki sha, jibi ki sami nunannun tumatur dinki manya guda biyu ko uku ki shanye, gata ki sha kankana ko nono. Ki dinga cin abu kala biyu a cikinsu, to wallahi Ina tabbatar mi ki banda ni’ima, hatta fatar jikinki sai ta murje ta goge ta yi kyau.Sabon Bidiyon Da Mallama Juwairiyya Bintu Usman Tayi Akan Ma'aurata

Sannan wasu daga cikin su a na shan ruwansu domin ni’ima ta musamman ko a sarrafa wani abin da ruwan, don samun dauwamamman jin dadin ma’aurata, kamar:

Ruwan kwakwa

Ruwan zam zam

Ruwan kankana

Ruwan tumatir

Ruwan zogale

Ruwan ruman

Ruwan ayaba

Ruwan guaba

Ruwan dabino

Ruwan rake

Inibi

Ruwan kwai

Ruwan kaninfari

Ruwan itacen baure

Ruwan sassaken gamji

Ruwan madarar shanu

Ruwan zaitun

Ruwan tuffa

Shan ko wane ruwa daga cikin wadannan ya na saukarwa da mace ni’ima mai kyau, mai kauri da yauki irin wacce maza su ke so, kuma ko wanne ruwa akwai yadda a ke sarrafa shi da mahadan da za su sa mai gida sambatun dadi.

Ga kadan daga cikin yadda a ke sarrafa wasu ruwan daga ciki:

.

(1) Ruwan Kankana, Ayaba Manya Uku, Kankana Kwata da Tuffa: Ki hada ki markada ki zuba madarar ruwa gwangwani daya, zuma yadda ki ke so, ki sa kankara ya yi sanyi, ku sha kamar juice ke da maigida. Ya na karin ni’ima da kaurin maniyyi.

Post a Comment

Previous Post Next Post