Yadda Zaka Kwashe Komai Na Tsohuwar Wayarka Zuwa Sabuwa How To Transfer All Your Data From Old One To New Phone

 Yadda Zaka Kwashe Komai Na Tsohuwar Wayarka Zuwa Sabuwa (How To Transfer All Your Data From Old One To New Phone)



 zaka tura dukkanin wasu abubuwan dake cikin tsohuwar wayarka zuwa sabuwar wayarka.


Yana da wuya kaga mutun ya chanja waya ace ya taho da komai da yake cikin tsohuwar wayarshi zuwa cikin sabuwar, amma anan zaka ga yadda ake transfer na komai harda messages da calls.


Koyon wannan dubarar ko ince wannan ilimin yana da matuƙar muhimmanci sosai a garemu baki 'daya.


Ko kasan mafi yawan mutane suna fasa siyan sabuwar waya domin gudun kada su rasa wasu abubuwa da suke a cikin tsohuwar wayarsu? To kaga idan ka kasance mai sayarda waya zaka iya tabbatar masu da bazasu ta6a rasa komai da yake cikin tsohuwar wayarsu ba, domin su sayi sabuwar waya a hannunka.

Sabon Bidiyon Mallama Juwairiyya Bintu Usman Akan Ma'aurata Danna Nan Domin Karantawa

A wasu wuraren abun kasuwanci suka 'daukeshi, idan mutun ya sayi waya sabuwa zaka ga an kira wani an bashi wayoyin duka biyun wato sabuwar da tsohuwar ance yayi transfer na kayan dake ciki, kuma daya kammala ya kawo zaka ga an sallameshi ku'din aikinshin.


Tabbas idan ka koyi wanan ilimin zai amfaneka harma ya amfani wasu da suke a kusa dakai ta hanyar nesan taku daga yin asarar wani abunku na cikin tsohuwar wayarku dan wai kun chanja sabuwar waya.


Ga yadda abun yake...


Da farko zakaje cikin playstore na kan wayarka kayi download na wannan app 'din 'SMART SWITCH' akan duka wayoyin guda biyu. Idan wayoyin Samsung ne kuma sai kayi search na 'SAMSUNG SMART SWITCH' shine wanda yake aiki akan Samsung kuma yana aiki akan wasu Android 'din amma bai cika yi akan wasu 'dinba.


Bayan kayi installing na app 'din a duka wayoyin guda biyu, sai ka shiga daga cikin shi app 'din domin fara yin transfer na kayanka.


Zai nuna maka wasu za6u66uka guda biyu kamar haka 'SEND DATA' da kuma 'RECEIVE DATA' anan fa sai ka lura da kyau, ita wayar da kayan naka suke aciki wato tsohuwar itace zaka danna 'SEND DATA' a kanta, ita kuma sabuwar wadda kake da buƙatar tura kayanka zuwa cikinta itace zaka danna 'RECEIVE DATA' a kanta.


Haka shima mataki na gaba zaizo maka da za6i guda biyu kamar na baya amma shi zai nuna maka 'CABLE' da kuma 'WIRELESS' cikin sauƙi sai ka danna 'WIRELESS' 'din.


Daga nan kuma zaka danna next ka wuce mataki na gaba wanda zai nuna maka inda zaka za6i abubuwan da kake son turawa suma kamar haka...

Calls and contact

Messages

Apps

Settings

Home screen

Images

Videos

Audios

A wannan wajenne zaka za'bi abunda kakeson turawa a sabuwar wayar taka, idan kuma duka kake da buƙatar ka tura sai ka duba daga samansu akwai wani waje da aka rubuta 'All' sai ka danna shi, zaiyi maka mark na duka abubuwan, sai ka danna next domin ya fara transfer 'din, zaka jira na wasu 'yan lokuta kafin ya kammala amma ya danganta ne da adadin nauyi da yawan abubuwan da suke a cikin tsohuwar wayar taka amma baya daukar wani lokaci mai tsawo sosai.


Matakin gaba sune da kansu zasu gaya maka cewa transfer 'dinka ya kammala kuma sun tattara maka dukanin wani abun da kayi transfer sun aje maka a fuskar screen na wayarka, zaka ga inda suka rubuta maka 'Go to home screen' sai ka danna wajen, kai tsaye zai kaika inda abubuwanka suka sauka, haka kuma zaka ga adadin girman abubuwan da ka tura zuwa cikin sabuwar wayarka 'din, wato 'Data transfer results.


Masha Allah.

Zaka iya koya ma wasu domin suma su anfana da ilimin daka samu, ko kuma kayi sharing dan wasu suma su gani kuma su anfana.

© Abu Ibrahim

Post a Comment

Previous Post Next Post