Wani Sabon Sirrin Man Zaitun Da Tafarnuwa Domin Ma'aurata

Wani Sabon Sirrin Man Zaitun Da Tafarnuwa Domin Ma'aurata.



Idan ka samu tafarnuwa ka bare bawon gaba daya, sai ka sanya tafarnuwar a cikin wata kwalba mai dauke da MAN ZAITUN a ciki sai ka rufe.

Ka barshi a rufe har tsawon sati biyu, sai ka rika shan babban cokali Uku (3) kullum da safe kafin kaci abinci.

Wannan hadin yana magance wasu cutuka da matsaloli kamar haka:

1🧄- Yana tace jini, da Yardar Allah.


2🫒- Yana wanke Hanta daga kitse ko wata matsala, da Yardar Allah.


3🧄- Yana kawar da tsakuwar dake cikin QODA da yaradar ALLAH.


4🫒- Idan har mutum yana shanshi to yana magance matsalar basur idan kuma basur din mai tsiro ne sai arika shafa shi a dubura.


5🧄- Idan matsalar ciwon gabobine ko sanyin kashi sai a rika shafa shi a wurin da yake da matsalar.


6🫒-Masu fama da matsalar zubewar gashi sai su rika sha kuma suna shafa wannan hadin a gashinsu


7🧄- Idan masu fama da matsalar LOW SPERM COUNT suna shan wannan hadin to da yardar Allah za su iya rabuwa da Matsalar.


8🫒- Kuma yana magance matsalar Infertility ( wacce take iya sanadiyyar samun jinkirin haihuwa) da yardar Allah ga maza da mata.


Wasu da dama sunyi amfani da hakan kuma Allah ya sa andace

"Tafarnuwar ta kasance kamar adadin yawan rabin kwalbar Man Zaitun din. Misali idan Man zaitun din 1Litre ne, to anaso yawan tafarnuwar takasance rabin lita (1/2 Litre). Allah yasa mun gane."

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. 

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.



Post a Comment

Previous Post Next Post