Amfanin Tsamiya A Jikin Dan’adam, Wanda Ba Kowa Ne Ya Sani Ba

 Amfanin Tsamiya A Jikin Dan’adam, Wanda Ba Kowa Ne Ya Sani BaKamar yadda ya kasan ce sanannen abu ne gurin mu Musulmi, ba wani icen da Allah (SWT) ya halitta face da irin ta sa fa’idar, sai dai ya kasan ce an gano wannan fa’idar ko kuma ba’a gano ta ba. Duk da tsamiya aba ce me tsami amma tana da abubuwa da yawa na karin lafiya , sannan tana kunshe da sinadaran kara lafiya da kuzari da sauransu.


A cikin dukkan kayan marmari tsamiya tana da ingantattun sinadaran iron, magnesium, niacin, phosphrous, protein, da potassium amma me ciwon siga zai yi kokarin kada ya sha saboda tana kunshe da sikari.


Har ila yau tsamiya tana da mahimmanci game da al’ada saboda ingancin abubuwan gina jiki da ta kuntsa.


Ciwon Mara lokacin Al’ada; Ana hada tsamiya da man zaitun dan a sha domi maganin ciwon mara na lokacin al’ada dama wanda bana al’ada ba. Ana shan tsamiya saboda kumburin ciki ko rashin bayan gida, ciwon hanta da mafitsara da kuma ciwon ciki.


 


Ana maganin sanyi da zazzabi, akan baiwa yara saboda tsutsar ciki. Akan sarrafa yayan tsamiya don maganin karaya. Ruwan yayan tsamiya na maganin bushewar ido akan disa shi a ido.


 


Wasu daga cikin amfanin tsamiya dai sun kunshi:


❑– Yaki don hana kamuwa da cutar ‘cancer’.


❑– Kariya daga karancin sinadarin ‘bitamin c.


❑– Saukaka ciwon zazzabi.


❑– Kariya daga kamuwa da mura.


❑– Taimakon jiki wajen narkar da abinci.


❑– Saukaka cushewar ciki.


❑– Ragewa jiki yawan kitsen ‘cholesterol’.


❑– Taimako wajen inganta lafiyar zuciya.


❑– Kurkura ruwanta na saukaka kaikayin makogwaro na mura.


❑– Dafaffen ganyenta na maganin ciwon ‘ulcer’ da taimakawa wajen kashe tsutsar ciki ga yara.


❑– Tana maganin basir.


❑– Taimako wajen tace jini.


Kazalika ana iya amfani da ita don magance cututtuka da dama, kadan daga ciki su ne:


★ Maruru.

★ Gudawa.

★ Amai.

★ Cututtukan hanta.

★ Kuturta.

★ Cututtukan fata.

★ Ciwon ido.

★ Guba.


Da dai sauran cututtuka.


Copyright BY: Sirrin rike miji

FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji

EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com

FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji

WhatsApp: ☏+2348037538596


 Message Sirrin rike miji on WhatsApp. https://wa.me/2349037075823

Post a Comment

Previous Post Next Post