Yawan Shan Tsami Ko Daci Ko Zaki A Lokacin Da Mace Take Da Juna Biyu

 Yawan Shan Tsami Ko Daci Ko Zaki A Lokacin Da Mace Take Da Juna Biyu 



 A duk lokacin da mace ta samu ciki, to, ta shiga cikin samun sauye-sauye kenan kullum a tsarin jikinta da kuma daukacin rayuwarta, har sai ta haihu. Daga cikin sauyin da take samu wanda ya shafi tsarin jikinta akwai tsananin bukatar wasu abubuwan ci ko sha masu dandano daban-daban. Wani lokaci ma zata ji tana tsananin bukatar cin abun da ba abinci bane, kuma zai iya cutar da ita kamar su kasa (sand), alli (chalk), gawayi (charcoal), datti (dirts), kai wasu ma har da kashi.


Sau da yawa mata masu juna biyu sukan so su ci ko su sha abu mai tsami, daci, zaki, bauri da sauransu. Yin mu’amala da wadannan abubuwan zai iya yi mata illa ga lafiyarta ko kuma abinda yake cikinta, musamman idan ta tsananta ci ko shan su.


TSAMI: Wasu daga cikin masu ilimin likitanci da kimiyya sun tabbatar da cewa yawaita ci ko shan abu mai tsami gamai juna biyu zai iya yin mummunan tasiri ga girma da kuma tsarin halittar jaririn da ke cikinta (genetic mutation), musamman a lokacin wata uku na farkon samun ciki (first trimester). Amma idan mai juna biyu ta ji bukatar ci ko shan abu mai tsami, to, yakamata tayi amfani da ’ya’yan itatuwa (fruits) ko kuma kayan lambu (vegetables) masu tsami, kamar su inabi (grape), tumatur (tomatoes), tsamiya (tamarind), lemun tsami (lemon), pineapple (abarba) da sauransu domin basu da wata illa. Yakamata mai juna biyu ta guji shan nono mai tsami, ko maganin gargajiya mai tsami.


DACI: Ci ko shan abubuwa masu daci ga mai juna biyu yana da hadari, musamman a cikin wata uku na farko (first trimester). Dalili shine suna iya haifar da takurewar mahaifa ta motse, daga nan sai ayi barin ciki (miscarriage). Misalin abubuwa masu daci sune shuwaka (bitter leaf), guna mai daci (bitter melon), sake-sakin maganin gargajiya (herbal concuctions) da sauran su.


ZAKI: Ci ko shan abubuwa masu zaki fiye da kima ga mai juna biyu yana da illa. Zasu iya haifar da ciwon suga ga mace wanda ake samun sa lokacin da ake da ciki (gestational diabetes). Wani nazarin ma ya nuna cewa zai iya sanyawa a haifi jariri da ciwon numfashi na asthma, ko kuma ya shafi kaifin fahimtar karatu ga yaro idan ya girma (intellectual memory). Kuma zai iya sanya yaro ya kamu da ciwon suga (daiabetes), ko kuma yayi taiba (obesity) idan ya girma. Misalin abubuwa masu suga sun hada da chocolate/sweet, abubuwan sha na kwalba ko gwangwani (processed soft drinks) da sauransu.


A gaskiya idan mace tana da ciki fa sai a hankali, domin abu kankani yana iya haddasa mata matsala ko kuma jaririnta. Don haka sai a ci ko kuma a sha tsami, daci zaki da sauran su kadan-kadan. Allah ya raba ku da cikkunanku lafiya kuma ya raya su bisa sunnah, amin.


WalLahu A’lam.

Post a Comment

Previous Post Next Post