Shin ko kasan kuka na kara karfin Azzakari Da Karin Ni'ima Ga Mata :

 Shin ko kasan kuka na kara karfin Azzakari Da Karin Ni'ima Ga Mata :





 Maganin Da Kuka Take Yi


Kuka tana maganin zazzabin maleriya.

Kuka tana maganin tarin fuka TB.

Tana kara ingana garkuwar jiki.

Kuka tana kara jini a jiki.

Kuka tana maganin gudawa.

Kuka tana maganin hakori.

Kuka tana maganin ulsa.

Kuka tana rage kiba.


Baya ga wadannan, malama Maijidda ta ce idan ana shan kuka ba zai sa mutum ya samu kumburin ciki ba saboda rashin narkewar abinci sakamakon sinadarin fibre da ke cikinta. Haka kuma ga wadanda ke son rage tumbi ana iya shan ganyen kuka domin yana narkar da kitse.


Masaniyar ta ce kuka tana maganin ciwon ulsa – “ga mai ulsa zai kada ganyen kuka a ruwa a sha, cikin lokaci kadan zai samu saukiin ulsa.”


Kuka Tana kara Ni’ima Ga Mata Da Mazakuta Ga Maza Masana sun ce, saboda tasirin kuka wajen inganta ruwan jikin mutum, tana kuma tasiri wajen kara ni’ima ga mata.


Yadda ya kamata mata su yi amfani da kuma a cewar malama Maijidda, za a samu sassakin kuka a wanke sosai sai dinga sha kofi daya da safe da yamma. Sannan ta ce, kuka tana kara wa maza karfin jiki da mazakuta. Haka kuma mazan da ke son jikinsu ya bude kuka tana taimakawa saboda sinadaran da ke cikinta.


Yadda Ya Kamata A Yi Amfani Da Kuka

Ana busar da ganyen kuka a nike a tankade a yi miya domin cin tuwon dawa ko masara ko shinkafa ko alkama. Kamar yadda aka yi bayani tun a farko cewa kuka tana da matsayi musamman a abincin Hausawa.


Hausawa suna yin miya da ganyen kuka. Ana busar da ganyen kuka a nike a tankade a yi miya domin cin tuwon dawa ko masara ko shinkafa ko alkama. Haka kuma Hausawa sukan yi amfani da kuka wajen yin danwake. Amma masana sun ce danyen kuka ya fi amfani fiye da busashen garin kuka da ake miya da shi.


Malama Maijidda ta ce, yadda ake busar da kuka yana kashe wasu sinadaran da ke kunshe a cikinta, saboda rana da aka shanya kukar tana kone sinadarai da dama.Ta ce danyen ganyen kuka ya fi amfani fiye da busashen garin kuka karin lafiya da sinadarai a cikin miya. Sannan ba a son idan za a yi miyan kuka a bari ta sha wuta sosai domin yawan dafuwa zai rage yawan sinadaran da ke cikin kuka, a cewar malama Maijidda.


Post a Comment

Previous Post Next Post