Yadda Ake Saduwa Da Mace Mai Ciki.
Wasu Na Ganin Kamar Idan Mace Ta Dauki Ciki Ba Za a iya Saduwa Da Ita ba.
Tambaya :
Malam na kanji wasu mutane na fadar cewa ba ya halatta idan
matar mutum tana da juna biyu yayi jima'i da ita har sai ta haihu meye gaskiyar maganar?
Karanta Wannan: Yadda Ake Gyaran Jiki Da Gwaiba
AMSA :
To dan'uwa ya halatta a sadu da mace lokacin da take da ciki, saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi : "Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to kada ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa" Abu-dawud : 1847
Ibnul kayim yana cewa : "Wannan hadisi yana nuna cewa ciki yana kara karfi duk lokacin da ake saduwa, saboda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kamanta shi da shuka, ita kuma shuka tana kara girma, idan aka ba ta ruwa" Tahzibussunan 1\193 .
Masana likitanci suna cewa: Ba'a so miji ya dinga hawa kan matarsa lokacin da take da ciki, zai fi kyau ta dinga yin goho yayin da za su sadu, ko kuma ya sadu da ita ta gefe, saboda kwanciya akanta yana iya wahalar da yaron .
Sannan yawanci mata basu cika son yawan saduwa ba idan cikinsu ya girma, wasu likitocin suna bada shawara cewa a karanta saduwa a wadannan lokutan.
Allah ne ma fi sani .
Post a Comment