Maganin Maikon Fuska Ko Jiki Ga Masu Yawan Maiko A Jiki Ko Fuska

Maganin Maikon Fuska Ko Jiki Ga Masu Yawan Maiko A Jiki Ko Fuska • Lemun tsami 

• Suga ko gishiri 

• Ki kwaba ruwan lemun tsami da suga kafin sugan ya gama narkewa ki riqa deba gina goge fuskan dashi. 

• bayan minti 30 ki dauraye da ruwan sanyi. Sau daya zuwa biyu a sati

 GA MASU YAWAN BUSHEWAN JIKI

 • Suga ko gishiri gwangwani daya • Man zaitun ko almond ko man cika gida (castor oil) rabin gwangwani 

• Zuma kwatan gwangwani

 • Lavenda oil ko wani mai kamshi chokali daya • Ki hada su wuri daya bayan kin gama wanka ki shafa shi ki dan dirje jikin ki dashi sannan ki jira minti biyar ki dauraye da ruwa ki fito 

• Wannan hadin zai kai tsawon sati biyu ba tare da ya lalace ba.

 GA WADANDA JIKINSU bashi da wata matsala, za su iya amfani da kowanne daga cikin wadannan biyun. 

4-YAWAITA SHAFA MAI Muatane da yawa basa son shafa ma ajikin su suna ganin cewa ba wata damua to akwai damuwa kokuma a shafa a kafa da hannu da fuska kadai shi yasa lokuta da dama sai kaga jikin mutum yayi dabbare dabbare ko ina kalarsa daban. Please mu riqa amfani da man shafawa masu kyau ban a bleeching ba.

 Idan kinyi amfani da wannan baki ji dadin sa ba kar ki kuma sayan irinsa ki nemi wani har sai kin samu wanda kka ji dadin sa daga nan sai ki cigaba da siyan irinsa. Sannan ya kamata mu san wannan:- 

• BODY CREAM KO BODY LOTION wannan a jiki kadai ake shafawa banda fuska shafa shi a fuska zai iya kawo matsala kamar na kunan rana, kuraje, da sauran su.

 • FACE AND BODY CREAM\LOTION wannan zaki iya amfani dashi a jiki da kuma fuska baki daya. 

Karanta Wannan: Hanya Goma Sha Uku Na Gyaran Fuska

• FACE\FACIAL CREAM wannan fuska kadai • Da sauran su.

 Al’muhim dai, mutum ya karanta rubutun bayanin da ke jikin mai sosai sannan ya duba kwanan watan da man zai lalace wato expiring date kafin ya saya.

 5-KARE JIKI DAGA RANA Rashin shiga rana yana daga cikin abinda yasa jikin yara yake da taushi da sheqi. Don haka duk lokacin da mutum zai fita ya riqa yawan amfani da sun protecting cream (SPF) ko kuma ki sanya nikabi. Musamman ga mata masu amfani da man bleachin rana zai iya kona fuskar ta zama ja idan basa neman kariya daga rana.

Post a Comment

Previous Post Next Post