Maganin sanyin mara mai tsanani na maza da mata.

 Maganin sanyin mara mai tsanani na maza da mata.

    


  MAGANIN SANYIN MARA DUK TSANANIN SA DA YARDAR ALLAH.


DON ALLAH IDAN KA KARANTA KA TURAWA SAURAN YAN UWA DOMIN SU ANFANA.


Matsalar sanyin mara matsala ce wacce take addabar mutane maza da mata masu aure harda wadan da basu da aure

Danna Nan Domin Karanta Amfanin Kuka A Jikin Dan Adam 

Kuma cuta ce wacce take shigar mutum ba tare daya sani ba sai bayan wani lokaci yayin sa ya fara ganin alamomin ta.

Ga kadan daga Alamomin cutar sanyin mara.

1. Dauke sha'awa: 

2. Fitar farin ruwa daga gaba: 

3. Tsagewar farji:

4. Fitar kuraje a gaban mace ko namiji

5. Saurin inzalii

6. Ciwon idanu,har yakan sa a daina gani

7. Fiyar kuraje a jiki ko wani sashe na jiki.

8.fitar kuraje a baki da makogaru 

Amma fa bacterial infection suna da yawa,amma mu masu maganin hausa duk suna daya ake kiran su dashi wato sanyin mara.

Amma a ilimin zamani na likitanci suna da sunayen su daban daban ga kadan daga cikin su 

1. Candida

2. Pelvic inflammatory disease(pid)

3. Gonorrhea

4. Urinary tract infection

5. Chlamydia

6. bacterial vaginosis

Wadan nan sune kadan daga cikin su,sai dai ta hanyar alamomi kusan baa iya banbancewa domin wasu lokutan suna da makamantan alamu,saboda haka aje ga likita domin sanin kalar wanda mutum yake dauke dashi

Amma ga kowannne a cikin su ga hanyar da zaa magance shi insha Allah.

ABINDA ZA'A NEMA:

1. Saiwar Zogale(Sayen zogale) da turanci kuma Moringa Root 

2. Tafarnuwa (garlic) 

3. Jar kanwa(potash) 

Da farko zaa samu saiwar zogale masu kyau zaa wanke ka samu kamar na #100 a zuba a tukunya sannan a kawo tafarnuwa dunkulen ta guda daya a bare shi,a daka sama sama,itama a zuba a tukunya,sannan jar kwanwa kamar karamin lemon tsami a saka duka da ruwa liter 

4. Sai a dafa sosai a sauke idan ya huce a tace a zuba a roba a adana a rika shan karamin kofi sau 2 a rana sati 2 idan cutar batai yawa ba,idan kuma tayi karfi ayi sati 3 zuwa wata 1.

Insha Allah zakai mamaki kwarai da gaske

Post a Comment

Previous Post Next Post