Yadda Zan Kare Kaina Daga Muguwar Kishiya

 Yadda Zan Kare Kaina Daga Muguwar Kishiya 


BOKA? 


Wai ke da kike da Manzon Allah, to har akwai wani Æ™azami can da zai iya burgeki? 


A wannan zamanin an yi wayewar da yakamata kowa ya ɗau haske waɗan nan ƙazaman bayan ƙarya ba abinda suke yi wallahi.


Eh tabbas akwai masu aiki da aljannu, to amma Allah ya haramta yarda dasu, kuma ko shi aljanin Allah bai bashi sanin me zai faru gobe ba wallahi. Amma abin takaici haka wata mace zata zuba zunzurutun maÆ™udan kuÉ—i a gaban wani Æ™azami wai don ya faÉ—a mata idan har ta bari kishiya ta shigo gidanta to zata hanata rawar gaban hantsi, zata rabata da mijinta, zata rabata da mijinta. Wannan duk abu ne da zai faru gobe Allah ne kaÉ—ai yasan me wannan kishiyar taki zata zo da ita. Amma haka wata mace zata zan kashe kuÉ—i tana ba wannan Æ™azamin ita Ala dole so take ayi mata abinda Allah bai mata ba. 



Babu wani wanda ya isa yayi abinda Allah bai yi ba. Wannan ne yasa ake kiransa da Ubangiji. Shi Giji ai sunan boka ne kafin kan mutane ya waye su gane wane ne Allah, to a lokacin da suka gane sai suka ce ga Uban-Giji wato ma'ana wanda ke yin abinda yafi na boka Giji kenan, Allah Subhanahu Wata'ala kenan.



Domin biyan buÆ™ata ko kowacce iri ce, to ki yi istigfari da salatin Manzon Allah kafin ki roÆ™e shi, sai kuma ki É—auka a ranki duk abinda ya faru muÆ™addari ne daga Allah, insha Allahu babu wata kishiya ko wani mugu da ya isa ya cutar dake. 

Post a Comment

0 Comments