Yadda Zaka Saurari Gidan Radio Na Kowane Jaha A Duk Inda Kake

 Assalamu Alaikum Abokai Barkanmu Da Yau, Fatan Kowa Ya Tashi Lafiya.


Yau Dai Bayaninmu Akan Yadda Ake Sauraron Gidan Radio Na Kowane Jaha A Duk Inda Kake Ne.Da yawan mutane suna son sauraron Radio amma basu san yadda zasu yi ba. To ga wata hanya mai sauki domin saura Radio na kowacce Jaha a duk inda kake fadin duniya. 


A kodayaushe cigaba samuwa yake yi, s can zamanin baya da ya wuce mutun ko yana son sauraron Radio sai dai ya sayi ita kanta Rakodar sauraran Radio, amma yanzu da wayarka ta hannu ma sai ka saurari gidan Radio Na Kowane Ƙasa kuma kowacce Jaha.

Bari dai kada in cika ku da surutu, ku karanci wannan gaba ɗaya domin fahimta.


Da farko ku shiga  play store ku sauke wannan supplication da zan baku. Bayan kun gama saukewa sai ku duba inda aka rubuta search sai ku taɓa daga nan sai ku rubuta sunan tashar da kuke son saurara ko kuma sunan Kasar da kuke son Saurara sai ku danna searching zai kawo muku jerin sunayen tashoshin daga nan sai ku shiga  wacce kuke ra'ayi. 


Amma fa kusani shi wannan application da data  yake amfani.

Danna NAN domin sauke application din


Post a Comment

Previous Post Next Post