Ni'imar Dake Cikin Kowacce Rana Kamar Yadda Ranar Juma'a Takasance Mai Ni'ima
 Ni'ima Da Take Cikin Kowacce Rana, Kamar Dai Ranar Juma'a.


Kowacce rana, tana da wata ni'ima wacce Allah yayi mata, amma mutane kadan ne suka san haka. Duk wata rana a cikin ranaku bakwai da wata ni'ima wacce Allah yayi musu tun daga ranar Litinin, Talata, Narba, Alhamis, Juma'a, Asabar da kuma Lahadi. Abu na farko da mutun zai gane hakan shi ne, babu wata rana da aka ware a cikin ranaku bakwai wanda aka ce ba za'ayi wata ibadar Allah a ciki ba saboda rashin rahamarta. Ni'imar Kowacce Rana.


Ranar Litinin (Monday)

Ranar Litinin (Monday) rana ce mai rahama da albarka. Ana samun dacewar yin

tafiya a wannan ranar. ldan mutum yayi tafiya a wannan

ranar zai samu nasarar abin da yake nema. Anaso ga wanda

zaiyi tafiya a wannan rana ya fara da yin sadaka.

Sannan ya karanta ayatul kursiyu da inna anzalnahu. Maka

ruhine yin tafiya a ranar Litinin din da ta zo daidai da kwanan wata 3, 4, 21

Da kuma 25. Ga watan musulunci sai dai idan da wani uzuri na

musamman. Kuma ya dace yayi sallar tafiya da addu'o'i idan haka ta kama

Ziyarar makabarta yana da tasiri sosai aranar Litinin(AL-AKHL

AQ WAL AADABUL ISLAMIYYA 928)Ranar Talata 

Falalar Ranar Talata: Tana daya daga cikin muhimman ranaku masu falala da daraja a kwanakin mako, ranar talata ranace ta biyan bukatu. Mai neman biyan bukata  yana cimma nasara a ranar talata. Ana yawaita arzikin mutumin da yake yawaita yin addu'a a ranar talata.

Wanda ake binsa bashi kuma bai samu abun biya ba to inyayi addu'a a ranar talata Allah Zai bashi abin biya. Wanda zaiyi tafiya ranar talata a naso yayi sadaka. Sannan ya karanta aytul kursiyu da lnna anzalnahu. Wanda yake da muhimmiyar bukata to yayi azumi aranar talata da laraba da alhamis. Yayi sadaka dai dai lokacin shan ruwa. Bayan yayi sallar magariba da isha'i yayi sujjada ya faɗa wa Allah bukatunsa. Zai ga biyan bukata da gaggawa da yardar Allah.
Falalar Ranar Laraba.  Tabawa ranar samu. Itama ranar Laraba muhimmiyar ranace mai daraja da albarka. Akwai karin magana da ake cewa kyakkyawar juma 'a tun daga laraba ake ganeta. Yazo a hadisi daga lmam Ali (A. s) yaana cewa shan magani ranar laraba yana gaggauta warkar da cuta kowacce iri ce. Makaruhi ne kirkirar tafiya ranar laraba sai idan da uzuri, amma ana kawar da kar hancinyin tafiya a ranar ta hanyar yin sadaka da addu'a bakin gwargwado. 


Falalar Ranar Alhamis: Alhamis rana ce da ba iya kimanta darajarta da ni'imominta dake a cikinta, rana ce maimatukar albarka da rahama. Idan mutum na da muhimmiyar bukata to sai ya yi salatin annabi dubu daya bayan sallar asuba ta ranar alhamis. Ya fadi bukatunsa insha Allahu buƙatarsa zata biya akan lokaci. Haka kuma mutummin da yayi azumin yinin alhamis kuma ya karanta fatiha da falaki da nasi da kulhuwallahu da inna anzarnahu da kursiyu da kuma ayoyi biyar na karshan surar Ali imrana to duk abin da ya roki Allah na alkhairi Allah zai biya masa bukatunsa.

Wanda ya shiga makaranta ko ya fara naiman ilimi a ranar alhamiss to zai dace da ilimi mai yawa da albarka, kuma zai rika fahimtar karatu sosai. Yin wanka

da yanke farce (akaifa) ranar alhamis duk abubuwane masu falala. Haka nan yin tafiya ranar alhamis akwai nasara da dacewa acikinta. Ana so mutum yayi sadaka. Kuma ya karanta ayatul kursiyu da inna anzalnahu a lokacin tafiyar tasa Ziyarar kabari ko makabarta yana da falala da lada ta musamman aranar alhamis. 


Falalar Ranar Juma'a


Ranar juma'a itaa ce rana mafi muhimmanci da daraja acikin ranakun mako. Rana ce ta idi da farin ciki ga musulmi. Rowayoyi da hadisai masu yawa sunyi magana kan falala da darajarta. Ba a ason yin fushi a ranar. Ba ason kuntatawa iyali. Musamman dukan yaro kada kuyi masa tsawa ba ason jin wakoki ko kade kade ko da na addinine. A ranar ba ason hirarraki marasa ma'ana ko yawaita dariya a ranar, anason kamewa da yawaita zikiri da salatin annabi.


anason yawaita karatun alqur'ani da addu'o'i i ko sau raransu ta hanyar Radiyo. Makaruhine ga mazaunin yin tafiya kafin sallar juma'a. Amma bayan salla abu ne mai kyau. Daura aure da bukukuwa suna da muhimmanci da tasiri a ranar juma'a. Don haka yinsu a wannan rana yana janyo albarka da ni'ima acikinsu.Falalar Ranar Asabar.


Nasara da Rabo ana samun dacewa acikin yin tafiya acikinta. Idan mutum yayi tafiya ranar asabar zai cimma nasara burin da yake da shi anaso ga wanda zaiyi tafiya ranar asabar ya fara da yin sadaka sannan

yakaranta ayatul kursiyu da inna anzalnahu ya kammala da addu'ar neman dacewa da cimma nasara sai dai in asabar din ta dace da rana ta uku ga watan musulunci ko 4, 2, 1, 25, ga wata

to ankarhanta yin tafiya acikinsu saidai in wani uzuri Allah yana amsa addu'o'i ya biya bukatar duk wanda ya roke shi

bayan fitowar ranar safiyar ko wacce asabar.
Falalar ranar Lahadi 


Lahadi ranace mai falala da albarka. Ana

samun dacewar fara yin gini acikinta. Sannan duk abin da ya danganci dashe ko shuka ko kafa wani abu cikin kasa na tsiro ana dacewa in akayi shi ko aka fara shi awannan rana.

Domin karin bayani aduba wannan littafi Allah ya yafe mana kurakuranmu akan wannan darussan.(AL-AKLAK WAL

AADBUL ISLAMIYYAH 929) wannan sunan wata makarantar Islamiyya ce. 

Post a Comment

Previous Post Next Post