Abinda Na Shuka Hausa Novels Na Aysha Alhassan Dan Fulani




 ABIN DA KA SHUKA...





PROFICIENT WRITER ASSOCIATION


The ability to guide is what all writer can have,we proficient writer will share this quality.





Aysha Adam Alhassan dan Fulani



Gajeren Labarin



  Numfashina na shiga kokawar ja da Æ™yar, saboda yadda ya ke Æ™oÆ™arin barazanar barin jikina, hawaye masu É—umi suka fara kwaranya a kwarmin idona kamar an buÉ—e indararo.

   Kalaman Æ™awata Wasila suka shiga amsa amo a kunnuwana kamar a yanzu take mini su 'Duk abin da za ki yi a rayuwa ki tabbatar kin yi mai kyau da inganci. Ina tsoron kada watarana ki É—auki wuÆ™a ki daÉ“awa cikin ki. Kada kuma saÆ™on da kike aikawa ya dawo zuwa gare ki.'

   A lokacin ban É—auka maganarta zata iya zama gaskiya ba, domin ina sahun mutanen da suke tunanin Æ™oÆ™arin su zai sa su kare kan su, kamar dai yadda na zama É—aya daga cikin mutanen da suke cewa idan jifa ya tsallake kan su to ya faÉ—a kan uban kowa.

  

  Na Æ™ara fashewa da kuka mai yawa ina girgiza kaina "Kaicona! Kaicon wannan rayuwar tawa!"

    "Ki daina É“ata hawayen ki a banza, indai kuka ne yanzu kika fara yinsa, ki gama anan, kuma ki jira abin da za ki tarar a ranar gobe. Domin Allah kaÉ—ai yasan yaran da kika zama silar lalacewar rayuwar su. Yanzu ki jure wannan zafin na duniya ne. Ga wannan kuma takardar ki ce, na sake ki saki uku. Ba zan iya zama da macen da ta zama silar lalacewar rayuwar 'yata ba." Kalaman mijina suka zama kamar sauÆ™ar mashi a Æ™ahon zuciyata, abin da ya faru da ni ya zama kamar sharar fage ne a kan abin da ya aikata mini.

  Ashe kuskure nake ta yi? Ashe ban sani ba na daÉ—e da kashe rayuwata wajen neman birge mutane da son nema yi musu gwaninta.

   Wasu hawaye masu É—umi suka sake sauÆ™a a idona a lokacin da na ga mijina da na shafe tsawon shekaru ashirin tare da shi ya ja Æ™ofa ya fita ya bar ni, fitar da take nuna mini cewar ya fita a rayuwata har abada kenan, ban kuma iya tsayawa na dakatar da shi ba saboda nauyin haÉ—a ido da shi ma nake ji.

   A lokacin faÉ—an iyayena ya sake dira a kunnuwana suna tirr da Ala wadai da É—abi'ar da ta zama shamakin raba igiyar aurena da mijina.

  A lokacin na ji inama dai ace mutuwa ce ta É—auke ni, inama ace a lokacin da na yi mummunan gani numfashina ya bar gangar jikina. To amma idan na mutu a irin wannan lokacin na ce wa Ubangijina me? Me na samu a duniyar me kuma na tara na fuskantar sa? 

   Wani magiji mai Æ™arfi ya haska a idanuwana inda ya dawo mini da jiya zuwa yau, rayuwata ta jiya ta ci gaba da haskawa a cikin idanuwana a lokacin da gangar sheÉ—an ke kaÉ—a mini shi da mabiyansa ina musu rawa.


***

 Sunana Hassana Adamu Hussaini, tun ina matashiya nake karance-karancen litattafan Hausa, har zuwa lokacin da na yi aure da mijina Abdullahi, yakan kawo mini su ina karantawa litattafai ne masu É—auke da darasi da wayarwa da mutane hankali a kan zamantakewar rayuwa. 

  Har zuwa lokacin da na haifi yarana guda huÉ—u, Zulfa'u ita ce É—iyata ta farko wadda nake matuÆ™ar so da Æ™aunarta, sai Æ™annenta uku maza. Kasancewarta mace na É—auki Æ™auna da kulawa na É—ora a kanta.

  A lokacin zamani ya ci gaba da sauyawa har zuwa lokacin da rubutu ya koma a waya, marubuta da dama suka fara sharafinsu a yanar gizo, a lokacin na ji nima ya kamata na zama marubuciya, sai na fara rubutu mai kyau, sai dai kururuwar mabiyana da yadda suke zuga ni a kan na zuba gishiri da magi a kan rubutuna ya sa na karkata akalar alÆ™alamina daga neman mutuntaka zuwa neman É—aukaka.

  Kafin wani lokaci sunana ya fara yaÉ—uwa a media, har zuwa lokacin da na fara wani shahararren littafina mai suna Manyan Mata. Wanda ya kasance tsagaren lasbiyan na ke nunawa, kuma hakan ya samo asali ne da fina-finan banzan da nake sauÆ™ewa duk saboda kururuwar mabiyana da son birgesu.

  Zan iya cewa kwalliya ta biya kuÉ—in sabulu a lokacin, domin dubu É—ai-É—ai nake siyar da littafin, wasu kuwa masu son zama a zaure na musamman har dubu uku suke biya nake tura musu sau uku a rana.

   Labarina ya jijjiga duniyar sama, ko na ce yanar gizo, domin na samu mabiya ba adadi, gefe guda kuma na samu masu zagina da masu yi mini nasiha a kan na ji tsoron Allah. Ƙawata Wasila na É—aya daga cikin mutane masu mini nasiha amma na kawar da batunta gefe kamar yadda na fara zagin masu zuwa mini wa'azi, mabiyana na zuga ni da cewa hassada suke mini.

   Kwatsam tafiya ta kama mu ni da mijina, na bar É—iyata Zulfa'u 'yar shekaru goma sha takwas a gida ita da Æ™annenta saboda suna jarabawa a makaranta, mu kuma biki ake a dangin Abbanta.

  Tafiya ce ta kwanaki biyu za mu yi ta, na jaddada musu a kan kula da gidan ita da mai aikinmu Uwale, na ga farinciki kwance a fuskokinsu ban ga damuwa ba kamar yadda Zulfa'u take yi a wasu lokutan.

    Haka muka tafi cike da alhinin rabuwa da yarana, a kwana guda da tafiyarmu kiran Zulfa'u ya shigo wayata, ina É—auka ta fara tambayata yaushe za mu dawo duk da sanin na sheda mata kwana biyu za mu yi, kamar zan amsa mata a gobe sai kuma wani sashi na zuciyata ya hanani na ce mata zan kirata idan za mu taso, na ji murnarta da walwalarta a lokacin.

  Tunanina ya kasu da yawa na neman dalilin farincikinta da rashin zuwana kamar dai yadda nake neman me ya mantar da ita da ranar dawowar mu.

  

  Washegari ban sanar da ita muna hanya ba, amma tun da muka É—auki hanya na ke jin gabana na ta bugawa da Æ™arfi, na yi ta ambaton 'Inna lillahi wa inna ilahairraji'un!' Sau ba adadi a zuciyata, amma ban daina jin abin da nake ji ba, har zuwa lokacin da muka yiwa gidanmu tsinkaye muka dira da dirawa irin ta masu iko a kan sa, shigar rashin neman a ba da izini kafin a shiga.

   Æ˜irjina ya buga da Æ™arfi na ji kamar an sa majanyi an jani baya Æ™afafuwana suka sandare duk saboda mugun ganin da na yi a falon gidana.

   ÆŠiyata Zulfa'u ce tsirara mata kusan shida sun yanyameta kamar za su cinyeta a ciki har da Uwale mai aikina.

   Na buga Æ™ara da Æ™arfi ina nanata kalmar "Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un!" Da Æ™arfi amma kamar ba su duniyar da za su ji mu.

  Ganin halin da nake ciki Abdullahi ya Æ™araso, abin da ya yi tozali da shi ya sa shi yin bayana yana ambatan "Subhanallahi! A'uzubillah!" Yana rintse idanuwansa da Æ™arfi.

  Na yi kukun kura na É—auki taÉ“arya na shiga jibgar matan da ke cinye É—iyata, nan take suka dawo hayacinsu suka fara wawurar tufafinsu, na musu duka lilis kamar zan kashe su, anan na cakumi wuyan Zulfa'u kamar zan kai ta lahira.

   Da Æ™yar Abdullahi ya É“anÉ“areta a lokacin ta fashe da kuka ta na maida numfashi.

   Bayan shuÉ—ewar mintuna ashirin gidan ya rage daga ni da mijina sai Zulfa'u da Uwale, Abdullahi ya kalle ci cike da takaici "Wa ya koya muku wannan abin?"

  Anan suka yi shiru, har na zabura na sake rarumar waya sai na ji maganar Zulfa'u "A gurin momy muka koya wallahi, littafin da take rubutawa nima ina cikin group É—in da ta buÉ—e, na sauya suna zuwa Mom preety." Wayar da ke hannuna ta sulluÉ“e ta faÉ—i Æ™asa na zauna daÉ“as a Æ™asa kamar mutum-mutumi.

   "Yi mini bayani yadda zan gane." Abdullahi ya sake buÆ™ata.

    "Wayar momy na É—auka naga rubutun da take na fara karantawa, shine na ji ina son jin Æ™arshen, daga bisani na siyo kati na tura mata ta whtspp bayan na sauya sunana nace ina son littafin. Tun da na fara karantawa hankalina yake tashi, har nake son na ga yadda ake yi a zahiri watarana na ari wayarta anan naga bidiyon lalatar na tura a wayata, sanadin haka hankalina ya sake tashi har na tashi Uwale na gwada mata, daga nan muka fara yi."

   "To sauran fa?" Ya sake tambaya.

"A makaranta ne abin ya ciyo ni bayan karanta littafin nata, shine na je hostel nake yi da kaina, har ƙawata Zuby taga haka, ashe itama ta karanta littafin momy shine muka fara yi da ita, koda nace zan kwana a makaranta saboda jarrabawa ƙarya ne, da ƙawayenta ta haɗa ni suma 'yan lesbiyan ne. Shine fa muka jone tare."

    Maganarta ta Æ™are a lokacin da numfashina ya É—auke cak.

  

***

  Ban sake sanin abin da ya faru ba sai a yanzu da na ga mijina da takardar sakinsa, da kuma fita a rayuwata gaba É—aya.

   Lallai gaskiyar 'yan magana Abin da ka shuka shi za ka girba. Ina tunanin zan lalata yaran wasu ashe har nawa na lalata, yanzu wa gari ya waya? Babu aure babu mutunci babu kima, ga na rasa yarana. Na Æ™ara fashewa da kuka da danasani wanda na san ba ta da amfani.


  Ƙarshe.

Post a Comment

0 Comments