Yar Kwangila Page 31 to 35 By Mubarak A. Kamba Sadaukarwa Ga ArewacinNaija News Team

 




YAR KWANGILA.

_(hatsabibiyar yarinya)_

Mubarak A. Kamba

_(ramadan mubarak)_


Zamani Writers Association

(We're Here To Educate, Motivate and Entertain Our Readers).

PAGE 31 to 35


Cikin nasara da amincewar Ubangiji kowacen su ta samu damar kasancewa Æ´ar film da sahalewar iyayensu. Nana kuwa tuntuni ta samu Æ™aryata da tayiwa mahaifiyarta. Kamar yadda kullun a gidan Alh. Yusuf suka haÉ—e domin tsara komai. Yau ita ce rana ta farko da suka zauna domin tsara komai. Mallam Kabiru ya ce, "Wannan ita ce ranar raba aiki, saboda haka kowa ya saurari aikin da zai yi a cikin wannan aikin. Daga yau duk aikin da Kaci karo da shi ya zama aikinka a koda yaushe." Bayan ya gama faÉ—a musu hakan ya ja Æ™ofar bakinsa ya gimtse yayin da kowa ke zaune yana sauraron aikin da zai yi. "Alh. Yusuf ya ce,"Aikina shi ne neman duk wata alfarma a wurin manyan mutane kamar Æ´an kasuwa ko Æ´an siyasa ko kuma dai makamantansu. Nana, Zainab, Na'ima da Fadila aikinku zai kasance deceiving ne domin ire-iren waÉ—an da zamu na yaudara kyawawan Æ´an mata suke so. Likita kawo mana magungunan bacci ko mutuwar jiki ko makamancin haka ne aikinka. Mallam Salihu raba kayayyaki a gidan marayu da kuma sauran mallamai da masallatai ne aikinka. Usman kuma kamar yadda ka saba bincike wato leÆ™en asiri da kawo mana rahoto shi ne aikinka. Sai kuma Æ™arin Æ´an mata biyu wanda na rigada na sanar da su aikinsu tuntuni. ÆŠaya sunanta Malika aikin ta shi ne kwalliya domin É“atar da kama. Duk lokacin wata daga cikinku zata fita domin gudanar da aiki to akwai buÆ™atar ta sauya kamanni ta yadda ba za'a gane asalin fuskanta ba, wannan shi ne aikin Malika. ÆŠaya kuma sunanta Zarah." 


Yana kai aya suka yi ihu suna nuna farin cikin yadda aka rarrabi aiki cikin tsari, sai dai Nana ta fahimci wani abu da ba kowa ya fahimta daga cikinsu ba, wato aikin da Zarah zata yi, amma ba tace komai ba tayi gum da bakinta kamar yadda kowa yayi. Aikin da Zarah zata yi shi ne hacking na account duk mutanen da zasu yaudara. Dalilin da ya sa bai sanar da su aikin nata ba shi ne; aikin da zata yi mai matuƙar haɗari ne, wanda ba a son kowa yasan waye zai yi aikin don gudun tasowar wata matsala.


Alh Yusuf ya cigaba da cewa, "Task É—inmu na farko zai fara ne akan Mansur Barrister. Mansur Barrister wani matashi ne wanda bai gaza shekaru ashirin da biyar ba. Yaro ne fari tass dogo mai É—an jiki ba sosai ba. Mansur Barrister ya tashi ya tarar da tsabar daula a gidansu shi sam bai san wani abu talauci ba. Wannan ne ya sa yake yaudarar Æ´an mata ta hanyar É—aukar su yana kai su a É—akinsa yana fasiÆ™anci da su. Yayi lalata da Æ´aÆ´an talakawa da yawa kuma har yanzu ba wani hukunci da ya taÉ“a fuskanta duk da kuwa hukuma ta san abin da yake aikatawa, kasancewar mahaifinsa babban attajiri ne kuma lauya ne wanda  ba mai iya jayayya da shi ya kai labari. Ire-iren waÉ—annan matasan su ne babbar matsala a cikin al'umma shiyasa kawar da iri-iren su ba Æ™aramin taimawaka al'umma ba ne. Don haka zamu fara aiki ta kanshi ne." 


"To ina za mu fara, kashe shi zamu yi?" Nana ta faÉ—a. Mallam Kabiru ya ce, "A'a ai a wannan Æ™ungiyar tamu sam babu kisa, sai kuwa wanda ya taÉ“a yin kisa saboda haka ta abinda yake aikatawa ne zamu hukuntashi." 


"Kamarya ta abin da yake aikatawa, kenan muma fasiÆ™anci zamu yi da shi?" Na'ima ta faÉ—a taba zare ido. Dukansu hankalinsu yayi matuÆ™ar tashi tun kafin su ji yadda za su yi. "Ku kwantar da hankalinku ba kashe shi zamu yi ba, kuma ba wacce zata yi zina da shi amma kuma ba zai taÉ“a tsallake tarkon wannan Æ™ungiyar ta mu ba." 


"Mansur ya sakarwa Æ´an mata Æ´aÆ´an talakawa cutar HIV da yawa saboda shi ma yana É—auke da wannan cutar. Don haka da cutar HIV za mu hukunta shi. ÆŠaya daga cikin ku zata fara soyayya da shi, bayan soyayyar ta yi nisan da ba zai ji kira ba, Dr Hamza zai bawa wacce zata yi aikin Allurar jini mai É—auke da HIV ita kuwa zata É—ura masa jinin ne a jikinsa." 


Su duka su ka wani irin zuro ido waje suna ji a ransu wannan ba zai taÉ“a yiyuwa ba. Da Æ™yar Na'ima ta jawo linzamin bakinta ta ce, "Tayaya mutun naji yana gani za a É—ura masa allurar jini mai É—auke da cutar Æ™anjamau don kawai ya kamu da tsabar soyayya gaskiya wannan da sake." 


Nana ta buÉ—e baki  zata yi magana kenan, ya dakatar da ita ta hanyar É—aga mata hannu ya ce, "Tabbas haka za ayi ta hanyar yi masa allura mai É—auke da Æ™wayar Æ™anjamau ne kaÉ—ai zamu hukunta shi, amma kamar yadda kuka É—auka ba. Idan soyayyar ki ta yi masa katutu a zuciya ba abin da zai hana shi ya bi ki duk kuwa inda zaki kaishi, saboda haka a hotel zaki je da shi. A can ne zaki yi masa allurar bayan yayi bacci." "To tayaya zai yi baccin da har za a yi masa allura?" "Receptionist dake aiki a wurin shi ne zai kawo muku ruwan gora ko wani lemun shs mai É—auke da Æ™wayar bacci, idan kuwa har ya kuskura ya sha ruwan yayi baccin to daga wannan ranar zata kasance ranar lissafin kwanakin da zasu rage masa a duniya."  Cikin alfahari ya kai Æ™arshen maganar, wanda hakan yayi matuÆ™ar basu Æ™warin guiwa. A wannan karon ba su yi tafi da ihu ba amma sun yi matuÆ™ar jinjina masa. 


Yayin da kowa yayi shiru ana nazarin waye zai yi wannan aikin Na'ima ta ɗaga hannunta ta ce, "A bani wannan aikin zan iya." Hankalin kowa ya koma kanta. Mallam Kabir ya ce, kin tabbata zaki iya?" "Eh da yardar Allah zan iya, a bani aikin." Ta faɗa tana ƙara jin wani ƙarfin zuciya na ratsata.


"Ta ina zaki fara?" Alh Yusuf ya tambayeta. Sai da ta É—an yi shiru tana nazari kafin daga bisani ta ce, "Zan fara kulla alaÆ™a da shi ne." "Tayaya zaki Æ™ulla alaÆ™ar da shi?" "Zan fara bi ta hanyar da suke zama ne, a duk lokacin da zan wuce zan gaida su, sannan kuma zan dinga yin shigar banza. Nasan da wannan shigar zan ja hankalinsa gare ni."   


"Eh tabbas zaki iya, don haka babu wani É“ata lokaci cikin wannan makon zaki soma aiki. Nana zan turo miki kuÉ—i sai ku fara da shi kafin kammalawa." "Ok ranka ya daÉ—e muna jira." Nana ta faÉ—a. Zaman su na yau ya Æ™are. A lokacin da kowa ke Æ™oÆ™arin miÆ™ewa domin ficewa Fadila ta ce, "Bakuyi magana akan Film da zamu fara ba, ko kuwa shikenan ba maganar." 

Wani sabon zama ya sake samuwa kowanensu ya koma ya zauna. Abubakar Sale ne ya fara magana kafin wani ya ce wani abu ya ce, "Eh lallai wannan maganar mai muhimmanci ce yakamata mu tattauna akanta. Ni ne ya dace in fara maganar, amma sai kika fi ni bakin faÉ—a. Insha Allahu yanzu ba mu da matsalar registration kowa dake nan sunansa na cikin industry saboda haka ranar monday zamu fara training domin fara shooting." 


Ba Æ™aramin daÉ—i  Fadila ta ji ba. Haka sauran Æ™awayen nata sun yi farin ciki da jin wannan sanarwa. Alh Yusuf ya ce, "To ai ba mu san ma ya sunan Film da zamu fara É—auka ba, ashe har ka gama tsara komai, ko dai already kafin in kiraka ka shirya ne?" "A'a wallahi ba wani shirin da nayi kafin nan sai da ka kirani ne sannan na fara shirya komai, wannan ba wani abin mamaki ba ne idan ka samu Æ™wararrun ma'aikata. Sunan shirin da zamu fara É—auka shi ne HATSABIBIYAR YARINYA. Muntasir Shehu ne ya rubuta labarin wanda ni zan yi producing kuma zan yi directing." 


"Wow da kyau tabbas kam tsarin yayi kyau. So insha Allahu zamu bada haÉ—in kai domin fara wannan shirin cikin nasara duk da yake zamuyi wannan shirin ne domin manufar mu."

Daga nan taron ya watse kowanensu ya koma gida cikin aminci. A tsakar gida Nana ta tarar da Umma na surfe. Da gudu ta zo gare ta tana cewa, "La! La! La! La! Umma daka kike yi da kanki?" Kafin Umma ta yi wata maganar ta sake cewa, "Haba Umma koma mene ne ai ki jira zan dawo.". "Nadan da zaki dawo, amma ko kin dawo ai ke É—in ba yi zaki yi ba. Wai ma tsaya tun yaushe kika bar gidan nan kuma me kika je yi?" "Haba Umma na faÉ—a miki fa wannan kamfanin ne na Mblog. Interview ne ake yi tun safe sai yanzu mu kayi nasarar kammalawa." Ta faÉ—a cikin sanyaya murya tana kallon Umma da fargaban kada ta hanata. 


Sai da Umma ta yi murmushi sannan ta saki jiki. Umma ta ce, "To shi kenan yanzu sai ki É—auko taÉ“arya mu yi saurin gamawa." Ita ma murmushin ta yi ta ce, "Haba Umma na faÉ—a miki fa wannan kamfanin idan har na samu aiki a Æ™arÆ™ashin sa shikenan mun fita duk wani talauci. Wannan daka da kike yi ma ki ajiye shi kawai zan biya ayi." 


Umma dake riÆ™e  da taÉ“arya ta yi tana mamakin yadda lamari ke Æ™oÆ™arin zama É—an zani. "Shi kenan, yanzu kina nufin mun fita daga wannan talaucin kenan?" "Eh  Æ™warai kuwa Umma, ai na faÉ—a miki wannan kamfanin ba Æ™aramin kamfani ba ne insha Allahu daga yau rashi ba zai Æ™ara mana barazana ba. Yanzu nan ma zan je kasuwa in siyo mana kayan abincin na marmari da abin sha.


"To ikon Allah! Ni fa har yau ban yarda cewa wannan ahiriritar zai yi wani tasiri ba." "Ai kuwa Umma yau zan tabbatar miki da abin da nake faÉ—a."


Wucewa ɗakinta ta yi ta ɗauro wani ƙaramin zani ta wuce ban ɗaki don yin wanka. Bata wani jima ba ta yo wankan ta fito ta shiga ɗaki ta shirya. Tana gamawa shiryawa ta faɗa wa Umma zata je Kasuwa. Umma kuwa ta yi mata fatan nasara. A kasuwa ta shiga da kuɗi masu yawan gaske ta ɗebo abinci daban-daban. Buhun ahinkafar Ɗangote da magi kala-kala haka nan ta siyo doya da Irish da galaluwan manja kayan miya su albasa da dai sauran abubuwa da yawa waɗanda ake more rayuwa da su.


A titin dake layin Æ™ofar kasuwa ta samu wani É—an taxi ta É—uro kayan cikin motarsa su ka dawo gida. Kafin dawowarta gida ta haÉ—u da motocin  Faruk na ta wucewa akan hanya. Daidai lokacin da ya kawo kusa da ita ne ta ganshi a gaban mota ga kuma sauran motoci biye a baya da shi. Bayan sun É—an yi gaba kaÉ—an shi ma ya ganta ta cikin size mirror daidai lokacin da take Æ™oÆ™arin shiga taxi. Da sauri yasa aka dakatar da motar da yake ciki. Wanda ke jan motar ya ja hand break cikin firgici kaÉ—an accident ya faru a wurin kasantuwar tsayawar motar ba tare da shiri ba su kayi saurin juyowa kafin su dawo wurin mai taxi É—in ya É“ace ganinsu. Sama ko Æ™asa su ka rasa ta ina ya bi kamar aljani yayi saurin É“acewa ganinsu.


Sultan da ke baya da shi ya tambaya, "Wai kam lafiya tafiyarmu ta canja kai tsaye haka?" "Ba wani abu Driver juya mu je kawai." Faruk ya faÉ—a wanda hakan ya jefa Sultan da shi Direban matuÆ™ar mamaki. 


Nan take Nana suka isa gida yaran unguwarsu suka taya ta sauke kayan da tayo order daga kasuwa. A nan ta ciro kuÉ—i cikin Æ™aramar jakarta focs miÆ™awa mai taxi. Yana godiya ya karÉ“a don kuÉ—in da ta bashi sun fi Æ™arfin aikinsa. Haka nan ta ciro É—ari biyar ta miÆ™awa yaran da suka taya ta sauke kayan ta basu. Shigarta cikin gida ta tarar da Umma zaune kan tabarma tana karatun Qur'ani. 


Da ganinta ta ajiye karatun tana mata Barka da dawowa. "Wannan kayan Nana duk ke kika siyo mana." "Uhmmm Mama wannan fa ba wani abin mamaki ba ne, ai na faÉ—a miki idan na samu aikin nan zan yi matuÆ™ar baki mamaki." "Ai kuwa tabbas na yi mamaki. Allah yayi wa wannan aikin naku albarka, Allah yasa hakan ne mafi alkhairi." Umma ta faÉ—a tana riÆ™e haÉ“a. Dariya Nana ke yi sosai ta ce, "Ai Umma nan gaba kaÉ—an zamu je Makka da.." bata Æ™arasa ba wayarta ta yi Æ™ara ta yi saurin dubawa ta ga saÆ™on Na'ima ne. 

Tana fara karanta saƙon ta miƙe tsaye cikin fargaba.


Post a Comment

1 Comments