Mafarki Ne Ko Zahiri, Labari Mai Ciki Da Darasi

Mafarki Ne Ko Zahiri, Labari Mai Ciki Da Darasi



Na fara lura da cewa jikina yana canzawa, sai na fara jin daɗin kaina sosai, ina yawan tsayawa a gaban madubi na duba kaina. Har ya kai ga mahaifiyata ta fara lura da hakan ta yi min faɗa, don haka sai na koma ina duba kaina a madubin bandaki. A hankali, na fara jin daɗin tsayuwa a gaban madubin bandaki. Na fara son kallon jikina tsirara ba tare da wani dalili ba.

Bayan kusan watanni biyu ina yin wannan kamar yanda na saba, wata rana bayan na gama kallon kaina tsirara, na sa kaya zan fita, amma da na sake duban madubi sai naga wani mutum tsirara da yayi kama da ni daidai kamar hasana da usaini— kama ɗaya da ni amma namiji. Ya bayyana na ƴan daƙiƙu kuma sai ya ɓace. Amma abin da ya faru ya tsaya min a zuciya, bai barni ba.

Abin mamaki, ban tsorata ba ko ɗan kadan. Na ji kamar wannan mutumin ba baƙo ba ne — kamar na saba ganin sa. Bayan haka sai na fita daga bandaki na koma ɗakina domin in kwanta, saboda da safe zan tashi in tafi makaranta.

A cikin mafarki, na ga kaina ina tsaye a gaban layin metro. Babu mutane sosai. Sai wani jirgin metro ya tsaya a layin gefe, kuma daga cikin jirgin sai na ga mutumin nan da na gani a madubi. Ya tsaya yana kallona sannan ya sauka ya shiga cikin dogon bututun ƙarƙashin layin. Ya fara kirana da hannunsa, yana nuna in biyo shi.

Na ji kamar akwai wani abu da ke hana ni motsi, amma a ƙarshe na ci galaba. Da na fara tafiya zuwa gareshi sai na fara jin hayaniya — mutane suna ihu, jirgi yana danna hon deettt. Sai na farka daga mafarki da tsananin firgici. Na tarar da kaina tsirara, kayan jikina a ƙasa, kuma ga jini a jikin su

Na yi ihu da ƙarfi, mahaifiyata ta shigo ɗakin. Ta rarrashe ni, da adduoi bayan na dawo hayyacina. Na ba ta labarin duk abin da ya faru. Sai ta ce min:

— Na daɗe ina faɗa miki ki dena tsayawa a gaban madubi, amma ba kya saurara. Tashi ki sa kaya ki yi sallah kafin ki fita. Idan kika dawo sai mu je wurin Sheikh Bilal don ya yi miki rukiyta.

Da ƙyar na sa kaya, amma ban iya sallah ba saboda na manta. Na fita in nufi makaranta, Da safe ne, ƙarfe takwas, lokacin sanyi, babu mutane a tashar metro. Na fara tuno mafarkin… tashar daidai take da ta cikin mafarki!

Na tsinci kaina ina tafiya zuwa gaban wata mota ta farko ta tsaya. Kamar an ɗaure ni, na kasa juyawa. Sai metro na ɓangaren ƙetare ya zo, amma babu wanda ya sauka. Na ga wani allon talla a jikin jirgin, yana cewa: "Ke tawa ce, saura mataki ɗaya."



Ku Danna Wannan Rubutun Domin Karantawa 

Na kara jin tsoro. Sai na ji karar jirgin da zai zo a ɓangaren da nake tsaye. Ina kusa da gefen layin. Sai na ji wani tsoho yana cewa yana ja da ni:

— Ki yi hankali yarinya, wannan ne karo na uku da na same ki kusa da layin haka a cikin wannan wata. Ki kula da kanki.

Na hau metro ina mamakin kalamansa: karo na uku? Ni kuma? Me ke faruwa da ni? Nayi hauka ne ko aljani ne ya shiga jikina?

Cikin motar metro sai na ga allon da ke bayyana sunayen tashoshi kamar yadda ake gani a filin jirgi. Amma bayan sunayen tashoshi sun ƙare, sai allon ya sake rubuta kalmar nan: "Ke tawa ce, saura mataki ɗaya."

Na kara tsorata. Jirgin ya tsaya a tashar makaranta — amma duk tafiyar daga inda na hau har zuwa nan bai ɗauki fiye da daƙiƙa guda ba! Shin ta yaya aka wuce tashoshi 14 a daƙiƙa?

Na sauka ina rikice. Na shiga ajin mu, amma hankalina baya nan. Da aka gama sai na koma gida. Duk abin da ya faru da safe, ya maimaita kansa da yamma. Duk daƙiƙa ɗaya, tashoshi 14 sun wuce. Da na koma gida na shiga ɗaki na kulle kaina.

Sai na ji ana buga kofa, mahaifiyata na cewa:

Ke ba zaki tashi ki je makaranta ba?

Na ce:

Taya zan tafi?

Ta ce:

— Ai ke kika ba ni labari cewa kina mafarki da wani abu. Na ce miki ki tashi ki sa kaya, ki fita, sai mu je wajen Sheikh idan kin dawo. Na fita daga ɗakin ki don na shiga bandaki, da na dawo sai naga kin kwanta, se na kyal ki.

Maganarta ta bani mamaki. Ban iya cewa komai ba. Bayan ta fita, sai naga mutumin nan ya bayyana yana fuskantata yana cewa:

— Gobe ne ƙarshe … zan jira ki a tashar.


Ya ɓace. Sai na ƙara ihu. Mahaifiyata ta shigo tana cewa:

— A'a, wannan abu ba za a sake yin shiru akansa ba. Yanzu zamu tafi wajen Sheikh Bilal.

Muka tafi. Da muka isa, Sheikh ɗin ya kalle ni da wani irin kallon mamaki. Ya sa hannu sa a kaina. Jikina ya fara rawar jiki, na kama bacci. A cikin halin baccin, sai naga mutumin nan da yayi kamar ni, yana kallona — amma ba ya motsi.

Na farka da jin muryar mahaifiyata tana cewa:

— Tashi mana, har yanzu kina barci. Ki shirya ki je makaranta.

Na ɗauki wayata, sai naga har yanzu rana ce ɗaya da ta gabata – har yanzu 13 ga wata ne. Na ce da kaina:

Shin mafarki nake cikin mafarki? Ko kuwa abinda ya faru da ni gaskiya ne?

Na ce kawai zan yi ƙoƙari in manta da komai, in rayu da gaskiya. Ko mafarki ne, ko gaskiya ne — duk wahala ce.

Na sa kaya na tafi tashar metro. Na tsaya ina jiran metro. Sai naga jirgin tsaye a bakin bututun. Sai naga tsohon da ya ja ni a baya yana cewa:

— Ki je wurinsa, hakan yafi miki.

Na kalle shi, sai na kalle mutumin nan mai kama da ni. Sai naji wani hannu yana tura ni da ƙarfi. Na kasa tsayawa, har sai da na faɗa cikin layin. Mutumin nan yana ciki yana murmushi. Na ji ƙarar mutane suna ihu. Na ji hon din jirgi. Na ji kukan mahaifiyata… sannan jirgin ya buge ni.

Wannan takardar ce da na samu a cikin ɗrwar ɗiyata bayan mutuwarta. Ina so in isar da wannan saƙon: Kada kowacce uwa ta rasa ɗiyarta kamar yadda na rasa tawa. Ku guji tsayawa a gaban madubi — domin sakamakon shi ba zai taɓa kasancewa alheri ba… zai kasance mutuwa…

Post a Comment

Previous Post Next Post