Wani Sirrin Dake Cikin Jima'i Wanda Wajibi Ne Ga Ma'aurata Su Sani

Wani Sirrin Dake Cikin Jima'i Wanda Wajibi Ne Ga Ma'aurata Su Sani




A yan shekarun nan matsala jima'i na daga cikin matsalolin da suke lalata rayuwar aure. Ire-iren matsalolin sun hada da rashin yin jima'i shi kansa, rashin lafiyar gaba, sirihi, tasirin pornography wato blue film da sauran su. Amma a yau, ina so nayi focussing ne akan matsalar da pornography ya haifar a wannan zamanin. yarkeji 

A Yau yana wahala ace akwai saurayi matashi ko yarinya matashiya da basu taba kyella ido akan wannan fim na badala da ake kira da blue film ko porn ba. Kusan duk a cikin mutum 10, to 8 zun taba kallo, ko dai so daya, ko sau biyu, ko ma fiye da haka. Wasu ba sun kalla bane da niyyar ci gaba da kallo, ko don suna so. Sun kalla ne watakila saboda sun ji wani yayi zancen, ko kuma sun ci karo da shi wajen kallon fina-finan Amurkawa, ko kuma don kashe kwar-kwatar ido (Allah ya tsare mu). 

Kusan ya zama al'ada yanzu, idan matasa za suyi aure sai sun kalla, ko dai saboda curiosity, ko kuma saboda neman ilimi, wanda kuskure ne hakan. Domin kuwa Malamai magabata sun tabbatar mana da cewa lamarin jima'i lamari ne daga Allah, kuma dan Adam baya bukata a koya masa, Allah ne yake bada ilimin idan lokacin yayi. Shi yasa idan ka balaga abu na farko da kake fara gani shine mafarki kana saduwa. Porn ba shine ya dace ya koyarwa kai ilimin jima'i ba, saboda haka ne ma nake so a cikin wannan rubutu na bayyana mana wasu abubuwa da yawa da muke ji, ko muke gani, ko ake fada game da jima'i da kuma illar da porn ko blue film yake bari a kwakwalwar mutane.


Alamomi Shida 6 Na Gamsuwar Macce

Kallon wannan fim na badala ya canja mindset din matasa da yawa, kai har ma da wasu manyan. Domin kuwa yanzu ana iya samun mace ta koka akan cewa mijin ta baya iya gamsar da ita yadda take so. Ko kuma namiji yaji a ran sa idan bai laga-laga da mace ba, to bai cika namiji ba. Ko kuma wasu suji, ai kai ba jarimi bane sai idan zaka iya hour kaza, ka kayi jima'i a dare sau kaza, shine ka cika jarima. Hakan nan idan kaje kasuwanni magani, da chemists, za kayi ta cin karo da maza suna karbar magunguna Manpower don zaburar da kawunan su. Su ma matan ba'a bar su a baya ba, domin kuwa basa zama ba tare da sun sha ko sun ci wani abu makamancin wannan ba. Bana manta labarin wata baiwar Allah da muka kashe auren ta saboda mijin ta yana shan magani manpower sosai, a rana maganar bakwai ake zuwa goma. Wallahi wannan ne sanadiyya mutuwar auren. 

Abin da mutane da yawa basu sani ba shine: Jaridar Cosmopolitan ta wallafa wani interview da tayi da jaruman blue film su 40. A inda bayanansu suka nuna cewa shi film din blue film ko porn, film ne kamar kowane irin film. Yana dauke da scripts, wato labari, action, fiction da sauransu. 70-85% na abubuwan da ake bayyana wa a porn ba gaskiya bace zalla, akwai zuki-ta-malle wato fiction. Za'a iya nuna jarimi da jaruma sun shafe hour daya zuwa biyu suna abu daya, amma a bayan fage, sun tsaya sun huta sama da sau biyar. To amma a camera an yanke don kar ka gani. Saboda haka ake so ka yarda. 

Suka kara da cewa, badan suna hadawa da magani ba, da ko minti 10 baza su iya yi ba, kuma ba don taimakon camera ba, da shima hakan bazai samu ba. Wata daga cikin wanda akai wa interview din ta kara da cewa, ko iface-iface da suke yi, saka su akeyi don karawa kallon armashi. Ta kara da cewa, wasun su, a cikin tsananin zafi suke, saboda abin ya wuce hankalin da kuma limit da jikin dan adam zai iya dauka. Don haka Director ne zai ta cewa ayi ta ihu don a inganta scene din da ake. Don haka ba gaskiya bane. Wani jarima shima ya tofa albarkacin bakin sa inda yace, shi mai aure ne, kuma tunda yake saduwa da matar sa, bai taba wuce min 20 ba. Wanda idan da kuwa a film ne, har mai hour uku yayi.  

Idan ka koma bangaren litittafen Hausa da Novels, suma sun taimaka kwarai wajen sanyawa matasa tutani makamancin wancen, da burika wajen mu'amalar auratanya. Wannan shima koma bayane sosai, domin kuwa mata sukan kalli mazajen su a matsayin malalata, ragwaye, marasa kuzari, saboda su a tunanin su, namiji shine wanda yake lasting minti 30 zuwa hour daya. Sannan bayan ya sauka, ya sake komawa, idan ya sauka ya sake, akalla sau uku ko hudu kafin Asuba. Tabbas akwai maza jarumai wadda zasu iya haka. To amma tambaya anan shine, meye matsayin hakan a lafiyance sannan da kuma addini?

Yazo a cikin Sahih Bukhari, Manzon Allah SAW yana cewa mu guji yin abubuwa over, domin duk abinda ya wuce hankali yana zama cuta ne ga dan adam. Jaridar PlayBoy ta Amurka ta wallafa wani bincike da tayi akan adadin mutanen da ya kai dubu hudu, a inda binciken nunawa cewa kaso 50% daga cikin participants din only lasted 9 minutes 40 seconds a lokacin saduwa. Kaso 30% kuma minti 14 da second 10. Kaso 20% kuma minti 20 daidai. Sai masana suka karkare cewa average mutanen duniya a yadda Allah ya tsara halitta, basa wuce minti 4 zuwa minti 9 a lokacin saduwa (Saduwa anan yana nufin sanda aka hade tirmi da tabarya). Sannan mafi yawancin mutanen duniya suna saduwa ne sau uku kacal a kowane sati. Kadanne daga cikin mutane suke saduwa kullum ko kuma fiye da sau daya a kowane wuni. Amma dai bayanai suna nuna cewa it is not normal dan adam yayi jima'i fiye da sau uku a wuni daya. Bayanai sun nuna cewa masu yin jima'i sama da 5 zuwa bakwai suna developing wata cuta mai sanya kwayayen da-namiji su fara fitar da jini a maimaikon maniyyi. Sannan yi din da yawa ta hanyar amfani da maganin sanya dadewa yana kawo mutuwar gaba ta dindindin bayan shekaru sun ja. 

Don haka ina so na ja hankalin ma'aurata da su sani cewa. Abinda suke karantawa a littafi ko suke kallo a film, ba wani abu bane illa shirin film ne kawai. Shirine don kayatarwa da nishadatarwa. Sannan binciken masana ya nuna kamar yadda yazo a mujallar PentHouse cewa ma'auratan da suke ta'ammali da porn basa iya gamsar da juna a lokacin saduwa. Jaridar ta kara da cewa, wannan matsalar tana haddasa mutuwar aure da 9% a kasar Amurka duk shekara. Sannan ta kara da cewa: bayanan sirri na porn industry sun nuna cewa industry din tana fuskantar kalubale na shara'a da mutane da dama wanda suka dauka cewa porn gaskiya ne, domin a cewar su, yayi destroying expectations na su kuma ya lalata musu rayuwar aure. 

Bari na dakata anan. Allah ya bamu ikon fadin gaskiya da kuma aiki da ita, ya kuma ganar da mu gaskiya duk rintsi, sannan ya kare mana idanuwan mu daga zinar ido.  

Post a Comment

Previous Post Next Post