Magungunan karin Ni'ima Don Ma'aurata:
Mai karatu, barka da warhaka kuma sannunmu da sake saduwa da kai a wannan makon. A wannna makon mu na dauke da bayani kan magungunan karin ni'ima ga ma'aurata, wato maza da mata. Wallafa wannan makala ya faru ne sakamakon yadda mata da yawa ke kuka dangane da rashin ni'ima da su ke fama da ita yayin saduwar aure.
Wannnan shafi na ku mai farin jini na ya dukufa don kawo mu ku ire-iren wadannan magunguna ne, don karin dankon zamantakewar aure tsakanin ma'aurata.
1. Kankana Uwar Ruwa.
Kamar yadda mu ka fada a sama ana samun mata da kan yi kukan rashin ni'ima, wanda hakan kan hana jin dadin jima'i tsakanin ma'aurata, sannan ya haifar da rashin gamsuwa tsakaninsu. Idan har kina fama da wannan matsala ko matar ka na fama da matsalar rashin ni'ima, sai ka karanta ka fada ma ta don ta hada, saboda a wannan harka ba kunya
Kayan Hadin Da Ake Bukata.
a. Ruwan Kankana, Kofi 1
b. Garin Dabino, babban cokali 3
c. Zuma, babban cokali 3
d. Madarar "Peak" rabin gwangwani.
Idan amarya ko uwargida ta tanadi wadannan abubuwa da mu ka ambata a sama, abin da za ta yi shine, za ta cakuda garin dabinonta da ruwan kankana da zuma, ta tabbatar sun gaurayu sosai, sai ta zuba cikin madararta, ta ke sha, da iznin Allah matsalarta za ta kau. Shi wannan hadin namiji ma zai iya amfani da shi.
2. Saka Mai Gida Kwakwazo.
Shi kuma wannan hadin, baya ga karin ni'ima da mace za ta samu, hakanan zai kara mata dadi yadda za ta iya gamsar da mijinta.
Kayan Hadin Da AKe Bukata:
a. Aya, babban cokali 5
b. Ridi, babban cokali 5
c. Cikwi, babban cokali 3
Yadda mace za ta yi wannan hadi shine, tun da farko za ta gyara ayarta, sannan ta soya ta, bayan haka sai ta daka ayar don ta samu garinta. Shi kuma ridi bayan ta gyara shi ta cire duk wani datti da ke cikinsa, sai ta nika shi don samun garinsa. Hakanan, shi ma cikwi za ta daka shi ne don samu garinsa.
Bayan ta samu garin wadannan abubuwa 3 da aka zayyana a sama, sai ta hada su waje guda ta gauraya su, ta tabbatar sun gaurayu sosai, sannan ta adana a mazubinta mai kyau.
Abu na gaba shine, ta samu madara ko nonon shanu mai kyau, sai ta ke zuba karamin cokali 2 cikin nonon ko madarar, ta ke sha safe da yanna a kowanne yini.
Samun ni'ima da gamsuwa yayin jima'i ba sai an fada ba.
3. Yau Dai-dai Na Ke Da Kai.
Wasu matan kan yi kukan rashin sha'awar jima'i. Akan samu mata da ke fama da wannan matsala da har ta kai ta kawo, a dole ta ke saduwa da mijinta, amma ba wai don ta na da sha'awar jima'in ba. Da iznin Alla idan ta yi wannan hadin ta yi amfani da shi za ta kasance mai sha'awar jima'i.
Kayan Hadin Da Ake Bukata:
a. Sassaken Baure, babban cokali 5
b. Kanumfari, babban cokali 3
c. Zuma, babban cokali 2
d. Lipton
Yadda za ta hada, za ta daka sassaken bauren bayan ta bar shi ya bushe don ta samu garinsa. Sai ta daka kanumfari, shi ma don ta samu garinsa. Za ta gauraya garin kanumfarinta babban cokali 3 da garin bauren babban cokali 5, bayan ta tabbatar sun gaurayu sai ta zuba zuma babban cokali 2 ta cakuda su, su cakudu sosai. Za ta debi karamin cokali daya na wannan hadi ta zuba cikin ruwan lipton ta sha sau biyu a rana. Sauran bayani mu na jiran amsar ki a sashen "Comment" na wannan shafi na "Lafiyar Iyali".
4. Na Fi Karfin Kishiya.
Kayan Hadin Da AKe Bukata.
a. Garin gero (Amma kar a surfa)
b. Garin furen(huda) tumfafiya babban cokali 3
c. Garin 'ya'yan zogale babban cokali 3.
Bayan an samu garin wadannan abubuwa sai a gauraya su, mace ta ke shan karamin cokali sau biyu a rana.
5. Saka Mai Gida Tsalle.
Wannan wani hadi ne da ke kara ni'ima a gefe guda kuma ya na motsa sha'awar jima'i. Kayan da ki ke bukata don hada wannan hadin karin ni'ima sune, Zuma mai kyau marar hadi, garin habbatus saudah, da kuma man zaitun. Yadda zaki yi wannan hadin karin ni'ima shine, za ki samu mazubinki mai tsafta, sai ki zuba garin habbatus sauda ciki, tun da yake mun san ruwan zuma na da kauri da kuma danko sai a zuba ta kan garin habbatus sauda ki gauraya su hadu sosai, sannan sai ki kawo man zaitun ki zuba ki kara cakuda su, ki tabbatar sun hadu sosai.
Idan ki ka tabbatar ya hadu sai ki samu mazubinki mai tsafta ki zuba ki adana. Za ki ke shan babban cokali daya safe da yamma. Wannan hadi na karin ni'ima kwarai da gaske.
6. Ni da Ke Mutu Ka Raba.
Wannan wani hadi ne mai saukin hadawa, sai dai kuma babban hadi ne, sakamakon yadda yake kara ni'ima ga mata yayin saduwar aure, kuma ya na tayar da sha'awar jima'i, kuma ya na kara santsi kwarai da gaske. Abin da ki ke bukata anan shine kanumfari kadai. Za ki jika shi ne ki tabbatar ya juku sai ki rinka sha akai-akai kuma ki na yin tsarki da shi.
7. Na Yafe Mi Ki.
Wani hadi ne dake kara wa mata ni'ima sannan kuma ya na motsa sha'awa. Abubuwan da ake bukata don hada wannan hadi su ne, ganyen zogale, zuma, kanumfari, madarar 'Peak' ta ruwa.
Idan ki ka samu ganyen zogalenki sai ki gyara shi ki cire duk wani yayi da ba'a bukata, daga nan ki wanke shi ki markada ki tace shi cikin mazubinki mai tsafta da ki ka tanada. Shi ma kanumfarinki za ki daka shi ne, don ki samu garinsa. Sai ki zuba zuma a cikin ruwan zogalen ki gauraya su hadu sosai, sannan sai ki zuba garin kanunfari a ciki ki gauraya, sai ki kawo madara ki zuba ki ke sha sau biyu a yini, da safe da yamma kenan.
8. Yau A Shirye Na Ke.
Wannan hadin an yi shine don maza da mata gaba daya, saboda ya na kara wa namiji ni'ima sannan ya kara masa kuzari yayin saduwar aure, baya ga haka ya na kara sha'awa, sakamakon haka ne namiji zai iya amfani da shi.
Abubuwan da ake bukata don hada wannan hadi sune, huda ko furen zogale, sai kuma 'ya'yan zogalen, da kuma dabino, sai kuma cukwi da madara ko nonon shanu mai kyau.
Tun da farko ana bukatar a samu garin furen da 'ya'yan zogalen saboda haka sai a shanya su su bushe, amma fa za a shanya fure da 'ya'yan zogale ne a inuwa saboda idan aka shanya su a rana, wasu sanadarai da ke da matukar muhimmanci za su kone, kuma ba za'a samu tasirin hadin ba.
Bayan an samu garin fure da 'ya'yan zogalen, sai a daka dabinon da cukwi a hada su waje daya a gauraye, sannan a adana shi cikin mazubi mai tsafta da murfi. Sai a ke diban wannan hadadden gari a ke zubawa cikin madara ko nono ana sha sau biyu a yini.
9. Daga Ke Ba Wata.
Wannan hadi ya shahara wajen mata, kuma ya na da matukar tasirin wajen janyo hankalin maigida zuwa ga uwargida. Ya na kara ni'ima sosai, baya ga haka ya na taimaka wa wajen gamsar da mai gida kwarai da gaske.
Abubuwan da kike bukata sune, nonon rakumi da kuma ridi. Bayan kin samu ridinki sai ki gyara shi don cire yayi ko tsakuwa da duk wani abu da ba'a bukata, sannan sai ki nika ko daka ridin don ki samu garinsa ki adana a mazubinki mai tsafta da murfi. Wannan garin ridin za ki ke zuba wa cikin nonon rakumi ki na sha safe da yamma. Wannan hadi na da saurin saukar da ni'ima ga mace. Saboda haka duk mai son karin ni'ima sai ta jarraba wannan hadi na karin ni'ima.
Post a Comment