Ire-iren Kalaman Soyayya Biyar Wanda Yakamata Ma'aurata Suyi Amfani Dasu Don Faranta Ran Junansu
1. Ko da yaushe zan kasance a sashenki cikin yanayin mai kyau ko marar kyau, lokacin farin ciki ko kuma na bakin ciki, Ina Sonki
2. Tun kallon farko da nayi maka na gane cewa rayuwata tayi dai-dai da taka. Kaine zabin zuciyata ina son komai da ya danganceka
3. Haduwa dake shine kwaloluwa mafi rinjaye a cikin nasarorin rayuwata ta duniya, ina fatan karar da yau gobe da jibi dama duk sauran lumfashin da ya rage min a wannan duniyar tare dake, ko da kuwa kowa zai gujeni.
4. Rayuwata ta cika ta tumbatsa da sinadaran haske tun farkon haduwarmu, ka sani ka cike wani babban gurbi a cikin zuciyata wanda ko a mafarkaina ban taba mafarkin samun wanda zai iya cike shi ba. Ina sonka
5. Na shaki kamshin turaruka da dama a wannan duniyar amma har yau ban shaki kamshin da ya kai kamshin soyayyarki dadi ba. Na dandani zuma sugar da madi sai naji dacinsu yayin da na dandani zakin soyayyarki, so na da kike ya zame min tamkar lumfashi a duk sanda kika daina tabbas zan mace
Post a Comment