Ciwon Ciki Da Ciwon Mara Lokacin Al'ada

 Ciwon Ciki Da Ciwon Mara Lokacin Al'adabudurwa ko matar aure me fama da wannan matsalar

kisamu wadannan magungunan

1 garin hulba

2 garin habbatussauda

3 garin kiswatul Hindi

saiki hadasu waje daya ki zuba ruwa da Zuma aciki sannan ki dafasu idan ya dafu saiki ajiye wannam ruwan da safe ki debi karamin kofi kisha kafin kici komai anaso ki dafa Wanda zai miki sati daya kafin ya kare kin huta da wannan matsalar insha allahu

BAYANI DANGANE DA HAILA

Ana haihuwar yara mata da wasu kwayaye biyu (ovaries) wadanda ke kunshe da dubban kwayayen da ba su nuna ba (duba shafi a kan Halittar jikin namiji da macce). Bayan yarinya ta balaga, a kowane wata tana sakin kwai daya da ya nuna. Ana kiran wannan ‘saukar kwai’ (ovulation), kuma wannan na faruwa wajejen kwana goma sha hudu kamin soma al’ada. Idan kwan bai hadu da maniyyi ba sai ya mutu. A kowane wata mahaifa na shirya wa yiwuwar daukar ciki, kuma fata ta cikin mahaifa na zama da kauri da kuma taushi. Idan jikin macce ya gane cewa ba maganar daukar ciki, sai fatar da ke cikin mahaifa, tare da kwan su zama haila su fice ta farji.


Karanta Wannan: Ciwon Mara Akan Ya Macce

Ba za a iya ganin kwan ba saboda ya cika kankanta. Ana fara kirga lokacin haila daga ranar da aka fara, zuwa jajibirin ranar da za a fara wata al’adar. Zagayowar al’ada na canzawa, don zai iya kasancewa kwana ashirin da daya ko kuma ma zai iya kai wa kwana arba’in. Idan macce na al’ada, tana iya amfani da tawalin al’ada ko kuma fad, ko audugar al’ada don ta tare jinin da ke zuba. Kina iya yin amfani da littafin tsarin lokaci watau diary domin sanin lokacin da za ki fara al’ada. Ba dukan mata ne ke yin al’ada a kan lokaci ba, kuma lokacin fara al’ada ya bambanta. Wasu ‘yan matan na farawa tun da wuri (alal misali tun suna da shekara takwas), yayin da wasun ke dadewa basu fara ba. Haka ma, tsawon lokacin da ake dauka ana hailar ya bambanta daga macce zuwa macce.

Yawanci suna yin kwana biyar zuwa bakwai. Amma kuma wannan na iya sauyawa, don a wasu lokutan ba a kaiwa kwana biyar. Da zarar yarinya ta fara al’ada, zai dau lokaci kamin jikin ta ya saba. A shekarar farko mai yiwuwa ta ketare wata daya ko fiye da haka bata ga haila ba. Amma yau da gobe jikin nata zai saba.

Irin canjin da ake samu na yawan sinadarin (hormone) da jikin macce ke samarwa kamin lokacin yin al’ada, ko kuma a lokacin al’adar, mai yiwuwa ya shafi halin da macce zata nuna, ko kuma abinda zata ji a ran ta. Mai yiwuwa ta ji karin kuzari, ko kuma ta ji tana sha’awar namiji, ko kuma ran ta ya baci, ta ji kamar ta yi kuka, ko kuma ta rika yawan fushi a lokacin saukar kwai ko kuma jim kadan kamin ta fara haila. Mai yiwuwa nonunan ta su rika ciwo ko su kara girma; kuma a wasu lokutan wasu kananan kuraje kan fito a fuska. Wasu matan sun dara saura jin bambam a jikinsu a lokacin da suke haila. Kuma wannan na iya sauyawa a rayuwar macce. Ta haka ne mata ke sakin kwayaye har zuwa lokacin da suka daina haila. A yawancin lokuta hakan na faruwa idan macce ta kai karshen shekaru arba’in zuwa hamsin. Bayan wannan lokacin, ba zata kara yin al’ada ba, kuma ba zata dauki ciki ba.

Idan kina matukar jin ciwo a lokacin al’ada, ko kuwa

kina da wata damuwa, sai ki nemi shawara daga likitan da ki ka yarda da shi, ko kuma ki tuntubi kungiyar tsara iyali (Family planning Association, watau FPA a takaice).

Post a Comment

Previous Post Next Post