Yadda Zaki Gane Idan Aljani Ya Shiga Jikinki A Lokacin Da Ya Shiga

 Yadda Zaki Gane Idan Aljani Ya Shiga Jikinki A Lokacin Da Ya Shiga Kuma akwai na fili dana 'boye.

Gasu nan kamar haka:


ALAMOMI NA FILI


1. Ciwon kai marar jin magani.


2. Gujewa bautar Allah kamar Rashin son sallah karatun Qur'anic da sauransu.


3. Rikicewa wato yawan dimuwa acikin Sallah.


4. Jiri, da kasala ayawancin lokuta.


5. Ciwon wani bangare na jiki, Amma ko anje asibiti an auna ba za'aga komaiba.


6. Fa'duwa, da kuma yin Eihu da maganganu irin na aljanu.


7. Faduwar gaba mai tsanani.


8. Rikicewar Jinin al'ada.


9. Matsananciyar mantuwa da shiririta akan harkokin rayuwa.


ALAMOMI NA BOYE


1. Firgita da jin tsoro, musamman ma idan mutum yana zaune, ko yana tafiyashi kadai.


2. Rashin yin barci na tsawon lokaci.


3. Yawan farkawa cikin tsoro.


4. Dannau.. Wato mutum zai ga wani BAQIN ABU yazo ya danneshi. Kuma ko kayi Eehu ba za'a ji ba.


5. Namijin dare. Mace zata ga aljani yazo yana saduwa da ita..

 Acikin siffar mijinta, ko kuma wani mutum wanda ta sani.

Ko kuma namiji ya rika ganin aljana tanazuwa tana saduwa dashi koyaushe yakuma ji ya tsani yayi aure.


6. Mummunan mafarki. Kamar karika ganin kana fa'da da Macizai da karnuka, da sauransu.


7. Yawan fushi da 'bacin rai ba tare da dalili ba.


8. Yin dariya, kuka, ko Eehu a mafarki.


9. Mafarkin ruwa, jini, ko makabarta, ko mayanka, da sauransu.


Akwai wasu alamomin da muka ambata wasu ciwon yana haifar dasu don haka hanyar tambayoyi ne zamu gane inda matsalar take.

Post a Comment

Previous Post Next Post