Wani Sirrin Dake Cikin Gawayi Wanda Yakamata Kisani

 Wani Sirrin Dake Cikin Gawayi Wanda Yakamata Kisani GARGADI: normal gawayi na itatace amma banda na Lagos 

1) Yana da amfani wajen tsaftace gida da kuma warin jiki misali, idan wani lungu a gida yana wasu, za a iya sanya Gawayi a wurin, in kuwa jiki ne, sai a yi garin gawayin, an sanya a jiki.

2) Gawayi na hana kayan marmari lalacewa, abin da za a yi kawai shi ne a dama gawayin sai a tsoma kayan marmarin a ciki

3) Gawayi na taimakawa wajen cire sinadiran da ke da lahani daga cikin kayan abinci. Za a tsoma kayan marmarin cikin ruwan Gawayi

4) Gawayi na sanya hakora su yi haske idan aka yi amfani da shi wajen goge hakoran.

5) Gawayi na dawo da dandanon miyar da ake tunanin ta lalace, abin yi kawai shi ne a Jefa gutseren gawayin cikin miyar

6) Gawayi na taimakawa wajen rage yanayin lailayi da juya yayin da mutum ya sha nau’ukan magangunan da ke janyo irin wadannan yanayin.

7) Gawayi na da amfanin wajen maganin miki ( ciwo) a jikin mutum

8) Ana iya amfani da Gawayi wajen tsaftace gurbataccen ruwan sha

9) Gawayi na maganin Ulcer idan mutum yana cinsa akai akai

10) Ana amfani da Gawayi wajen magance Cututtukan fatar jiki kamar kuraje da rigakafin gurbacewar jiki sakamakon cin wani nau’in abinci.

Post a Comment

Previous Post Next Post