Yadda Ake Hada Sabulu Na Domin Gyaran Fata Da Gyaran Fusmusammanka Da Kuma Hadin Dilka

 Yadda Ake Hada Sabulu Na Domin Gyaran  Fata Da Gyaran Fusmusammanka Da Kuma Hadin Dilka



1) DOMIN KYAWUN FUSKA


     A samu:-

1 . Garin zogale

2 . Farar albasa

3 .Sabulun ghana 

4 . Sabulun Dettol

5 . Sabulun salo


Yadda za a hada. 


Ki samu sabulun ghana dana salo dai dai kai daya sai ki samu dettol shima kamar guda 2 sannan sai ki sami garin zogale cokali 2 sai albasa manya guda 2 duk sai ki hada su a turmi ki kirbe su sannan sai ki juye a roba mai murfi zaki dunga wanke fuskarki da shi yanada kyau sosai yana magance kurajen fuska. 


2) HADIN DILKA


1 . Dilka da sukari

2 . Lemon tsami

3 . Man zogale

4 . Turaren Du'aul jannah 


   Yadda za a hada:-


Zaki zuba duk kayan a cikin ruwa sai ki sa wuta amma kadan har sai ya tafasa yayi kumfa sai ki sauke idan ya huce kirinka dangwala kina shafawa a ko ina a jikinki, ki bari ya bushe, zai fara murmushewa da kansa sai ki karasa murje shi sai kiyi wanka da ruwan dumi, fatarki zatayi kyau


3) SABULU NA MUSAMMAN

  A samu:-

1 . Madarar turari

2 . Lalle da dilka 

3 . Ganyen magarya

4 . Kur kur 

5 . Dudu osun da Detol

6 . Sabulun ghana


a hadasu wuri daya a daka su a turmi mai kyau su hadi jiki sosai sai ki runga wanka da shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post