Abubuwa Takwas 8 Dake Hana Mata Jindadin Jima'i Ko Rashin Sha'awa

 Abubuwa Takwas 8 Dake Hana Mata Jindadin Jima'i Ko Rashin Sha'awa 

Shin kana mamakin dalilin da ya sa iyalinka bata da sha'awa? Ko kema kina mamakin mai ya sa baki jin dadin jima'i ko baki da sha'awa? Sai ku duba ku gani mai yiwuwa wannan bayanan za su iya baku haske akan matsalar da ke damunku domin neman mafita.


Duk da yake anfi ganin cewa mata sun fi maza yawan sha'awa da son jima'i a yanayin halittarsu akan maza, ba abin mamaki bane a sami akasin haka wani lokacin, cewa akwai mata da yawa wanda ba Su da sha'awa ko kwadayin jima'i saboda wasu dalilai na lafiya.


 Hakan na faruwa inda zaka sami mace na gudun kwanciyar aure ko bata damu da ayi kwanciyar ba ko kada ayi (duk daya ne a gurinta) saboda ko da an yi ma bata jin dadin jima'in sam , ko kuma ba ta jin dandanonsa irin yanda ta ke tsammani ake ji , kamar yanda sauran mata 'yan uwanta ke jin dadin rayuwar aure da mazajen su. Tana yin kwanciyar aure ne kawai a matsayin wani aiki (duty) na biyan bukatar mijinta ba bukatar taba, kuma ba don tana jin dadi ko gamsuwa ba sai dai kawai don bautar aure ko gudun fushin sabawa al'ada, ko kuma domin kare mijinta daga fadawa tarkon zina. 

Karanta Wannan: Yadda Ake Hadin Dauwamammiyar Ni'ima 

Hakika akwai mata da yawa da su ke cikin wannan yanayin rayuwar aure marar dadi, wanda sun hakura da hakkinsu na jin dadin aure inda wasu matan kuma ke kokarin neman mafita daga wannan matsala ta neman hakkinsu daga mazajensu ko neman magani, koma kokarin fahimtar matsalar dake hana su jin dadin da nufin neman warwarar matsalarsu. Wannan kalubale ne babba.


Anan zan ari wasu bayanan lafiya domin bayar da gudun mawata a kan wannan sabgar ko bayani akan wasu daga cikin dalilan da ya sa wasu mata ba su da sha'awa, ko basa jin dadin jima'i (salam suke ji), ko basa jin dadi sosai, ko kuma ma basu taba jin dadin ba a rayuwar aurensu. Wasu dalilan fa na da alaka da macen, wasu kuma namijin ne. Sune kamar haka:


1. CIWON SANYIN MARA KO MATSALOLIN MARA DA MAHAIFA: Kama daga sanyin mara (vaginities/toilet infections, UTI & STDs), yoyon fitsari, 'kululun mahaifa (fibroid), da sauran cututtukan al'aura na daga cikin abubuwan da ka iya hana mace jin dadin jima'i.Misali, sanyin gaba mai zuwa da 'yan 'kananan kuraje cikin farji ko na sanya mace ta ji zafi wajen jima'i yayin saduwa, wanda sau da yawa masu kurajen basu ma san su na da kurajen ba cikin al'aura, sai dai suce su na jin zafi lokacin saduwa. Kurajen suna fashewa saboda da gugar zakari, sai wurin ya zama rauni. Hakan nasa mata tsoron jima'i da ganinsa abin azabtarwa gare su mai maimakon abin jin dadi. Sau tari basu san abinda ya haddasa zafin ba, wanda kuma mai yiwuwa ciwon sanyi. Ciwon sanyi na iya dakushe sha'awar mace ko namiji. Ciwon sanyi na iya haddasa bushewar gaba (vaginal dryness) wanda alamunsa shine daukewar ni'ima da 'kaikayin gaba. Idan gaba ya bushe zai yi wahala mace da miji suji dadin jima'i in banda zafi. Haka kuma shima 'kululun mahaifa (fibroid) ya kan ci karo da zakari cikin farji sai mace ta ji wani irin yanayi marar dadi (discomfort) lokacin nishadin aure. Kuma yana danne mahaifa ya hana haifuwa da kuma sanya yawan zubar jini. Don haka neman magani shine mafita.


2. BUDADDEN GABA: Rashin tsukakken farji yanda zai damki zakari da kyau domin samar da jin dandanon fata-da -fata a matse. Budadden gaba kalubale ne dake sanya raguwar jindadi tsakanin ma'aurata. Sau da yawa ma'auratan biyu ba zasu sami gamsuwa ba da kyau, sa'annan macen ba za ta iya jin 'kololuwar dadi ba (orgasm). Akwai dabarun kwanciya da magani na zamani da zasu iya magance wannan matsala.


3. KACIYAR MATA (WUCE GONA DA IRI WAJEN YINTA): kaciyar mata (female circumcision) wacce Wanzan ya yanke beli da yawa fiye da yanda ya dace. Yin hakan na kashe sha'awar mace idan ta girma. Da yawa mata an yanke musu sha'awa a duniya tun lokacin da suna jarirai. Wasu al'adun a duniya suna yanke beli ne kadan, wasu kuma kamar rabi ne ake fillewa, wasu kuma cire shi suke duka, wato yanke shi suke gaba daya. 


Yanke beli da yawa ko duka matsalace dake hana mace jin dadin jima'i, domin kuwa beli (clitoris) shine matattarar jin dadin jima'in mace. Kamar yanda dai Malamai sukai bayani cewa yin kaciyar mata Mustahabbi ne a Musulunci, Sharia kuma tayi nuni da cewa kada a wuce gona da iri wurin yankan, ba kamar yanda wasu wanzamai ke aikatawa ba yanzu. To sai a nemi bayanan Malaman Sunnah domin fahimtar mas'alar baki daya. Bugu da kari, za'a iya neman magani domin inganta jin dadin aure.


4. MAGUNGUNA : Ko shakka babu akwai nau'in magungunan turawa ko gargajiya da zasu iya dakushe sha'awar mace, misali magungunan da ake bayarwa domin rage ciwon damuwa ko tsananin 'bacin zuciyar mutum (antidepressants) da sauransu. Kina mamakin cewa ada kina da sha'awa amma yanzu shiru ne toh mai yiwuwa wannan maganin da kike sha wata da watanni , ko cikin satin nan , shine ke sace miki sha'awa. Yana da kyau duk maganin da aka bawa marar lafiya a asibiti ko wani wuri yasan tutsun maganin ("side-effects" nashi) don kada wani abu ya dameshi bai san abinda ya jaza masa ba.


5. RASHIN INGANTACCEN ABINCI MAI LAFIYA: Idan mace bata cin abinci mai kyau ta koshi wanda zai inganta lafiyarta da jikinta da sinadarai na ni'ima ,to sha'awarta tamkar shukace wacce bata samun ruwa wacce zata mutu. Kifi, naman kaza, madara, yogat, hanta, kwai, zuma, dabino, aya, gyada, kankana, ayaba da sauran abincin mai gina jiki da kuzari tare da 'ya'yan itatuwa zasu iya cika mace da sha'awa da ni'ima bayan 'daukewar sha'awa. Wadannan abubuwa marmari da abinci tamkar taki ne da ruwa ga shuka, wato sha'awar 'ya mace. Don haka mazaje su siyama matansu kayan dadi domin moruwa daidai gwargwadon hali.


6. SAURIN INZALIN MAIGIDA/ SAURIN KAWOWA/RASHIN KARFIN MAZAKUTA: Wannan matsalar nada alaka da mazajen aure kai tsaye. Wannan matsalar na cutawa mata sosai kuma wani lokacin tana da alaka kai tsaye da rashin karfin mazakuta. Idan akwai karfin mazakuta ga namiji koda ba babba bane zakarin zai iya gamsar da iyalinsa idan akwai karfi sosai, kuma zai dade yana saduwa da iyalinsa har ta biya bukatarta. Haka kuma idan muka kalli matsalar ta wata mahangar, hakan na faruwa ne saboda rashin sha'awar namiji - wato sinadaran jima'insa (sex hormones /low testosterone) sun ragu ko sunyi 'kasa , ko kuma hawan-jini ko ciwon-suga suke haddasa masa matsalar ko ma yawan sinadarin kolesterol ko wasu matsalolin zagayawar jini. . Don haka cin abinci mai inganta lafiya da harkar jima'i ko magani mai kyau da likita yayi izini dashi zai iya gyara matsalar. Mafi yawan lokutta mata na bukatar tsawon lokaci kamin su kawo (kololuwar dadi /"orgasm") sabanin lokacinda maza da dama ke iya jurewa su biya musu bukata. Don haka, yin wasanni , yiwa iyali wasa tsawon lokaci (foreplay) na iya fansar lokacin da mai gida baya iya kaiwa ta yanda mace zata iya fara biyan bukatarta ko kawowa kamin saduwa da ita ta.


7. RASHIN FAHIMTAR YANAYIN JIKIN MACE DA BUKATUNTA NA KWANCIYA : Ko wace mace da irin bukatunta na jima'i , akwai irin abinda take so ayi mata da na'uin kwanciyar da take jin dadinta amma da yawa kunya na hana mata bayyana abin da suke so, don haka sai subar mazajensu cikin duhu suna ta kokarin jarraba abubuwanda ba sa yi musu. Don haka matan aure su fidda kunya domin tattaunawa da mazajensu akan abinda suke so wajen jima'i da mazajen suma su bayyana irin bukatun nasu domin fahimtar juna da jin dadin rayuwar aurensu. Haka kuma yana da kyau mai gida ya rinka lura da nazari akan bukatun wasu sassan jikin matarsa idan mai yawan kunya ce. Yau da gobe zai iya gane abinda ke yimata wajen saduwa. Yau da gobe zaka tara ilimi mai yawa akan bukatar matarka amma idan har kana lura da kyau.


8. WASA DA GABA: Idan mace na wasa da farjinta (istimna'i) da yatsa ko wani abu ta take sakawa, zai iya sanyawa taji bata jin dadin jima'i ko gamsuwa da maigidanta sai tayi istimna'i saboda tafi kowa sanin jikinta da mallakarsa, ta gano bukatunta na shaidan wanda aurenta ba zai iya biya mata ba. Musamman bainar zawarawa da 'yan mata wannan abune game gari, da yawa sun saba biyama kansu bukata kuma zai iya shafar tarayyarsu da mazajen da zasu aura nan gaba. Kamar dai yanda muka yi bayani a wata wallafar mu a can baya cewa, istimna'i nasa wuyar kawowa ga mace wajen jima'i (dalilin koyama jikinta da sai an taɓa wani sashen farji don ta kawo, wanda mai yiwuwa ne zakari baya taɓa wurin lokacin saduwa - a zahirin jima'i. Don haka istimna'i yana sa rashin gamsuwar jima'i ga mace - mijinta zai sha wahala wajen gamsar da ita. Jikinta ya riga ya koya, tayima kanta horo. Zata ringa tunanin mijinta baya iya gamsar da ita ko mazaje data aura, saboda sabon da tayi da koyama jikinta hanyar gamsar da kanta fiye da hanyar da ta dace, wato jima'i a cikin sunnar aure. Ta canza dabi'ar ta. Da yawa zaka samu cewa mata masu yawan istimna'i basu jin daɗin jima'i sai istimna'i, koma basu gamsuwa sai sunyi istimna'i a bandaki bayan saduwa da mazajen aurensu. Wannan zai iya kawo babbar matsala a cikin aure.


Allah yabamu cikakkaar lafiya

Post a Comment

Previous Post Next Post